Bayani Game Da Ciwon Yatsa Na Dan Kakkare: Abubuwan Dake Kawoshi, Alamominsa Da Yadda Ake Maganinsa (Whitlow)

Ciwon dan kakkare


Dr. Don Allah meke kawo ciwon yatsa da ake kira kakkare wanda yake fitowa a dan yatsa na hannu ya rika zugi? Wasu har lalle suke sa masa koshin hakan nada illah?


Amsa

Ciwon kakkare yana É—aya daga cikin cututtukan da Æ™wayoyin cuta ke kawowa. Kuma yana É—aya daga cikin waÉ—anda ke addabar mutane da dama a cikin al’umma. Wasu sukan kwatanta shi da ciwo irin wanda ba su taÉ“a ji ba a rayuwarsu saboda azabar zafi da zugi.      

Ƙwayoyin cuta ne ke shiga tsakanin fata da farce (Æ™umba/akaifa) a dan yatsa sai su hayayyafa su samar da ciwo da kumburi. Ciwon Dan Kakkare akan samu wanda bakteriya kan kawo, akan samu wanda Æ™wayar cutar fungus kan kawo, akan kuma samu wanda Æ™wayar cutar birus kan kawo. Ana kiransa Whitlow ko kuma Felon a turance. 

Ya fi kama mutanen da ba su yawan tsaftace hannunsu ta hanyar wankewa da sabulu akai-akai, da kuma mutane masu yawan cin yatsa, domin kwayoyin cutar bakinsu suke sakawa a wurin, sai su hayayyafa su kawo ciwon. Haka kuma Dan Kakkare na iya shiga idan mutum ya samu rauni a yatsa, ba tare da kula da raunin yadda ya kamata ba.

Dan Kakkare


Alamomin Ciwon Yatsa Na Dan Kakkare 

Dan yatsan da dan kakkare ya shafa kan kumbura ya ɗuri ruwa ya fara masifaffen zafi ko zugi sosai, a wasu ma yakan fashe ko ya ɗaɗe. Akan samu iya samun kaluluwa a hammatar hannun da abin ya faru. Wani lokaci kuma ciwon na zuwa da zazzaɓi da zafin jiki da kuma hana mutum bacci saboda bala'in zugi.

Hanyoyin Kariya Daga Ciwon Yatsa Na Dan Kakkare 

1. Masu yawan cin yatsa ko farce dole ne su daina saboda suna cikin haÉ—arin kamuwa da wannan ciwo na dan kakkare.

2. Sai kuma jaddada yawan wanke hannaye da sabulu a kowanne lokaci.

3. Kula da raunin yatsa, ana son daga mutum ya samu rauni a yatsa komai ƙanƙantar sa kar yayi wasa dashi yaje asibiti domin samun magani. Dalili kuwa shi ne kwayoyin cuta masu kawo dan kakkare suna iya shiga ta wannan rauni, su maida raunin ya koma dan kakkare.

4. Da ciwon ya fara ya kamata mutum ya je asibiti inda za a gane ko wace Æ™wayar cuta ce ake ganin ta kawo masa dan kakkare, sannan a ba da maganin kashe zugi da na kashe Æ™wayoyin cutar da suka kawo ciwon. 

Yadda Ake Maganin Ciwon Dan Kakkare

Ana buƙatar mutum da ya fara samun wasu alamomin ciwon dan kakkare toh ya garzaya asibiti domin a bashi magungunan da za su taimaka masa. Ana bada magungunan rage raɗaɗin zafi da kuma magungunan antibiotics idan har ana tsammanin ƙwayar cutar bakteriya ce ta kawo dan kakkare.

Idan kuma ana tsammanin ƙwayar birus ce to ba'a cika bada magungunan antivirals ba, saboda cututtukan birus sukan warke da kansu, amma wani sa'ilin ana bada antivirals domin rage tsawon lokacin da ciwon zai ɗauka kamin ya warke.

Idan kuma yatsan ya kumbura ya É—uri ruwa, dole a je a cire ruwan da ya taru a asibiti kafin a ba da magunguna. Idan ba a cire ruwan ba yakan dau lokaci yana zugi. Idan kuma aka fidda ruwan, nan da nan yake bushewa da an fara shan magani.

Maganar kuma shafa lalle, ban sani ba ko cikin lalle akwai sinadaran da ke iya magance wadancan kwayoyin cuta da muka ambata madu kawo dan kakkare. Amma dai yafi kyau a guji sanya duk wani abu a raunin dan kakkare kar a je a saka wasu kwayoyin cuta na daban. Aje asibiti a karbi magani shi ne aula.

Jan Hankali:

Akwai wata hanya ta gargajiya da ake bi a wajen cire ruwan da ya taru a yatsan da ke fama da ciwon dan kakkare, wadda aje kira da sakiya. Cire ruwan da ya taru a yatsan dan kakkare abu ne nai kyau kamar yadda mukayi bayani a baya, amma cire su ta hanyar sakiya ba abu ne mai kyau ba. Yin sakiya yana da haÉ—ari sosai;

1. Rashin tabbatar da inganci da kuma tsaftar ƙarfen da ake yin sakiya dashi.

2. Rashin iya kula da raunin sakiya da kuma kare kwayoyin cuta daga ciki.

3. Akwai yiwuwar yaɗuwar ƙwayoyin cuta daga ƙarfen sakiya zuwa ga wanda za'a yiwa sakiyar, kamar irin su, kwayoyin virus na Hepatitis B da Hepatitis C, ƙwayar cutar Tetanus, da dai sauransu.

Na taɓa cin karo da wanda aka yiwa sakiya akan wani gyambo da ya fito masa, dalilin wannan sakiya ya kamu da kwayoyin cutar Tetanus wadda tayi sanadiyyar mutuwar sa cikin abinda bai fi mako ɗaya ba da yin sakiyar. Saboda haka a kula, idan har yatsa ya ɗuri ruwa, ko duk wani gyambo da yayi ruwan da ake ganin akwai buƙatar a tsiyaye, toh aje asibiti domin likita ya fasa.


Rubutu Masu Alaqa 

1. Shin Sabawa Da Istimna'i Yana Hana Mace Gamsuwa Yayin Saduwa Da Namiji?

2. Yadda Ake Kamuwa Da Cutar HIV Ta Hanyar Saduwa: Shin Ana Iya Kamuwa Bayan Amfani Da Baki?

3. Mene Ne TargaÉ—e Da Kuma Abubuwan Da Ke Hanawa Targade Warkewa (Ligament Tear)

4. Shin Matsala Ne Dawowar Ruwan Maniyyin Mijina Bayan Mun Gama Saduwa?

Post a Comment

0 Comments