Bayani Game Da Ruwan Nono Mai Maiƙo Ga Mai Shayarwa

Ruwan nono ga mai shayarwa


Tabbas akwai ruwan nono ga mai shayarwa wanda yana da maiƙo kamar yadda mata suke fada, saboda wannan ruwan nono yana ƙunshe da sinadaran kitse da kuma lipase wanda aikinsa shi ne ya narkar da kitsen da yake cikin ruwan nono ta yadda jikin jariri zai iya sarrafa shi idan ya sha. 

Akan iya gane ruwan nono ga mai shayarwa wanda yake da mai maiƙo ne idan aka ganshi da kauri kuma fari fat (thick and creamy). Ruwan nono garai-garai kamar ruwan sha ko kamar farau-farau, alama ce ta rashin maiƙo a cikin sa. 

Idan nonon mace mai shayarwa suka cika da ruwa (engorged), toh, maiƙon da yake cikin su zai ragu sosai. Sannan ruwan nono mai maiƙo yakan zo ne daga baya, ma'ana bayan jariri ya shanye ruwan nono da ba ya da maiƙo, nai kama da farau-farau, shi yasa masana ke kiran ruwan nono mai maiƙo da sunan hind milk.

Daga zarar mace ta shayarwa da jaririn ta kuma cikar nonon ya ragu, toh, ruwan nono mai maiƙon zai fara zuwa. Wannan ne dalilin da yasa ake shawartar mata da su daina saurin canja wa yaro nono sai ya shanye shi tas, idan ba haka ba, yaro zai sha nono maras maiƙo kenan. Alhali shan ruwan nono mai maiƙo shi ne ke gamsar da jariri daga barin jin yunwa, ruwan nono marar maiƙo shi kuma yana gamsar da shi daga ƙishirwa.

Ana so duk lokacin shayarwa mace ta baiwa jariri nono ɗaya kawai. Lokacin shayarwa ta gaba kuma sai tabashi dayan da bai sha da farko ba. Dalili kuwa shi ne, idan mace tana saurin canjawa yaro nono, toh ba zai samu shan ruwan nono mai maiƙo ba, sai dai yayi ta shan ruwan banza, saboda wannan ruwan nono mai maiƙo shi ne mafi amfani a cikin ruwan nono.

Alamomin Dake Nuna Jariri Baya Samun Shan Ruwan Nono Mai Maiƙo 

  • Tsumburewa da ramewar jariri.
  • Saurin kamuwar jariri da mura, ko zazzabi, ko rashin lafiya
  • Yawan kukan jariri, saboda jin yunwa 
  • Rashin walwalar jariri.

Hanyoyin Karin Maiƙon Ruwan Nono Ga Mai Shayarwa 

Ana son mace ta guji ɗurawa cikin ta magani sai ya zama dole. Mata masu matsalar yawan ruwan nono ko maiƙon nono suna tambayar maganin da yakamata su yi amfani da shi domin samun isasshen ruwa ko maiƙon nono. Maimakon haka, ga abubuwan da yakamata mace tayi:

1. Ta inganta yawa da darajar abincin da take ci, ta hanyar amfani da kayan marmari, proteins, da ganyaye.

2. Ta daina ɗaukar dogon lokaci ba ta shayar da jaririn ta ba, domin hakan zai sanya nonon ta su cika da ruwan nono sosai (engorgement), kuma cikar nono da ruwa sosai zai rage yawan maiƙon da yake cikin sa. Wasu masana suna da ra’ayin cewa idan ruwan ya taru kuma jaririn baya buƙata, toh, tana iya matsewa ta zubar. Amma ni bani da irin wannan fahimtar.

3. Mace ta riƙa mammatsa nonon (breast massage) domin yin haka zai zaburar da ɓuɓɓugowar ruwan nono mai maiƙon.

4. Akwai magungunan gargajiya masu haɓaka ruwa da maiƙon nono kamar hulba (fengreek), citta (ginger), tafarnuwa (garlic), da dai sauransu. Ba'a kyamar yin amfani da waɗannan a likitance. 

5.Sannan kada a manta da su farfesun kaza, ko na kifi, ko na kayan ciki. Ga kuma su kunun aya, kunun gyaɗa, zoɓo, da shayi mai kauri duk abokan tafiya ne. Magidanta sai a kula a saki bakin aljihu saboda matan mu su himmatu wajen yin ingantacciyar shayarwa. Allah yasa mu dace, amin. WalLahu Ta'ala A'alam.

Post a Comment

0 Comments