Ina mata da maza masu 'yan shafe-shafe? Ku fito yau gani na biyo ta kanku. A makon nan ne ƙaramin ministan lafiya na Nigeria, Dr. Iziac Salako ya koka sosai da yadda hukumar lafiya ta duniya ta ayyana Nigeria a matsayin ƙasa ta ɗaya a duk faɗin duniya wajen yawan masu amfani da mayukan koɗe fata, watau mayukan bleaching.
Dr. Solako yayi Allah wadai da masu wannan dabi'a, saboda tun ba yau ba anyi ittifaƙi akan cewa matan Nigeria su ne suka fi kowa amfani da mayukan koɗe fata na bleaching a duk faɗin Afrika. A inda wani bincike ya nuna su ne suka samar da fiye da kashi 70 a cikin ɗari (>70%) na masu yin bleaching a nahiyar.
A shekara ta 2015 gwamnatin ƙasar Ivory Coast ta hana shafa mayukan bleaching da duk wani mai da ke koɗe fata da ƙara wa fatar mutum fari, a wani mataki da ta ɗauka na kare lafiyar jama'ar ƙasar. Mata dayawa a Afirka, da wasu mazan ma, suna yawan shafe-shafe, ko kuma amfani da mayukan koɗe fata. Amma in ji ƙwararru, hakan na da illoli dayawa ga lafiya, cikin su har da ƙara haɗarin kamuwa da cutar kansar fata.
Me Yasa Hasken Fatar Mutane Ya Bambanta?
Kamin mu je zuwa bayani game da illolin yin bleaching bari muyi tsokaci game da me yasa muke ganin wasu mutane farare wasu baƙaƙe wasu kuma tsaka-tsakiya.
Allah ya halicci fatar mutane shimfida-shimfida (layer by layer), akwai manyan shimfida guda uku kamar haka:
- ShimfiÉ—a ta farko ana kiran ta da Epidermis
- ShimfiÉ—a ta biyu ana kiranta da Dermis
- Sai kuma shimfiÉ—a ta uku ana kiranta da Hypodermis
Zamuyi magana akan shimfiɗa ta farko kawai, wato Epidermis saboda ita ke da alaqa da haske ko duhun fata. Shimfiɗar Epidermis itama ta kasu zuwa shimfida biyar. Shimfiɗar Epidermis ta biyar wadda ita ce ta ƙarshe daga ita sai shimfiɗar Dermis, ana kiran ta basal layer ko Stratum Basale.
Wannan shimfiɗa ta basal layer ita ce ke ɗauke da tantanin halittun cells da ake kira melanocytes waɗanda ke samar da sinadarin melanin. Sinadarin melanin shi ne ke da alhakin sanya fatar mutum tayi baƙi. Gwargwadon yawan sinadarin melanin ɗin da fatar ka ke samarwa gwargwadon baƙin mutum.
Adadin tantanin halittun cells na melanocyte masu samar da sinadarin melanin ɗaya ne ga kowa, da baƙaƙen fata da farare har da turawa duk adadi ɗaya ne. Amma ana samun bambanci ne tsakanin yadda waɗannan halittun cells ke samar da melanin.
Halittun melanocytes na baƙaƙen fata sun fi samar da melanin dayawa, halittun melanocytes na turawa suna samar da melanin ɗan kaɗan, sai halittun melanocytes na zabya (albinos) basu samar da melanin gaba ɗaya saboda wani tangarɗa da ake haihuwar su dashi a ƙwayoyin halittar su.
Amfanin Melanin a Fatar Mutum
Wannan shi ne dalilin da yasa idan mutum ya cika shiga cikin hasken rana yake ƙara yin baƙi, saboda a lokacin da hasken rana ke dukan sa, jikin sa zai yi ƙoƙarin samar da melanin dayawa domin ya kare fatar jikinsa daga hasken, wannan ƙarin melanin ɗin sai ya ƙarawa fatar baƙi domin rage shigar hasken rana a cikin fata.
Saboda haka zamu ga cewa, baƙi da duhun da Allah ya bamu, alheri ne garemu ba abin kushewa ba. Wannan shi yasa zakuga cewa 'yan Afrika basu yawan kamuwa da cutar kansar fata kamar turawa.
Yadda Bleaching Ke Halaka Fata
Tunda mun ga abinda kesa fatar mu baƙi, kuma mun ga amfanin baƙin fatar mu, toh bari mu ga abinda mai bleaching ke yi. Idan mutum na bleaching yana aikata ɗaya cikin abubuwa biyu ne kamar haka:
- Ko dai yana koÉ—e fatar sa ta hanyar rage yawan halittun cells na melanocyte masu samar da malenin.
- Ko kuma yana rage yawan melanin É—in da melanocytes suke samarwa.
Kayan bleaching suna É—auke da miyagun sinadarai kamar irin su Hydroquinone, Mercury, Chlorides da Corticosteroids, wadanda illar su ba a fata kaÉ—ai ta tsaya ba, har da jawo ciwon koda da chanja wa mutum kamanni.
Illolin Bleaching a Mahangar Lafiya
1. Na farko kuma mafi hatsarin illar bleaching a fata shi ne ƙarawa mai bleaching yiwuwar kamuwa da cutar kansar fata. Kamar yadda muka yi bayani a sama mai bleaching yana halaka fatar sa ta hanyar halaka melanin ɗinsa da melanocytes, waɗanda ke bashi kariya daga cutar kansa.
2. Mayukan bleaching masu ɗauke da sinadarin Mercury (Hg) suna haifar da Mercury Poisoning a lokacin da ake yawan shafa su a jiki. Sinadarin mercury, yakan shiga cikin jini idan aka shafa shi a fata, idan yayi yawa a jini kuma yana iya hallaka ƙodar mutum nan take ya haifar da ciwon koda.
A ƙasar Amurika da sauran ƙasashen da suka san abinda suke yi, sun sanya doka mai tsauri game da amfani da mayuka da kuma magungunan da ke ɗauke da sinadarin mercury. Amma a Nigeria ana amfani dasu a matsayin ƙawa da magungunan bleaching ko kuma glowing ko gyaran fata kamar yadda wasu ke cewa.
3. Amfani da kayan bleaching masu ɗauke da sinadarin Hydroquinone suna sanya wani yanayin fata da ake kira ochronosis. Wannan yanayi na ochronosis shi kesa kaga fatar mai bleaching tayi wani fatchi-fatchi nan yayi fari nan ga wani fatchin baƙi, chan ga wani fatchin jaa. Kun ga a wurin neman ƙiba an kwaso rama.
4. Masu yin bleaching suna samun wata cuta da ake kira 'contact dermatitis'. Wannan cutar tana sanya fatar mutum ta bushe tayi ja ta fara yin wasu ƙuraje da ƙaiƙayi. Kuma suna iya samun ko wane irin kalar skin reaction.
5. Masu bleaching suna iya samun wasu ƙuraje da ake kira steroid acne, ma'ana ƙurajen bleaching. Mayukan bleaching masu dauke da Corticosteroids sun fu sanya waɗannan kurajen. Ƙurajen bleaching zaku gansu kamar kurajen pimples amma sun ɗan fi girma.
Idan sinadaran corticosteroids sukayi yawa a jikin mutum suna haifar masa da cutar Cushing Syndrome. Domin karin bayani game da Cushing Syndrome da yadda yake chanja kamannin mutum duba wannan rubutun 'Illolin Maganin Karin Kiba Na Sha Ka Fashe (Corticosteroids).'
6. Akwai wasu sabbin hanyoyin da ake amfani dasu ta hanyar shan kwayoyin magani ko allurai masu É—auke da sinadarai daban-daban da zasu hana jiki ya samar da melanin duk don ayi bleaching, mafi yawancin waÉ—annan magungunan da allurai suna da hatsarin gaske ba ma ga lafiyar fata kaÉ—ai ba.
Jan Hankali
Abin ban mamaki, a yayin da wasu yan Afirka ke yin bleaching domin komawa farare, wasu turawa su kuma tanning suke yi, ma'ana suna shan was magunguna domin komawa baƙaƙe don sun gano amfanin melanin a jikin fata, kuma sun tabbatar da cewa baƙar fata tafi farar fata daraja a kowane fanni na lafiya.
Kammalawa
Ya kamata mutane mu daina raina abin da Allah ya bamu na baƙar fata, haƙika alheri ne garemu kuma baiwa ne, saboda haka mu gode masa maimakon butulce masa ta hanyar yin bleaching.
Amma abin haushi, akwai wani gari a arewacin Nigeria mazan su har wani kirari suke suna cewa 'Duk wanda ya auri baƙar mace, toh kuɗin sa ne bai kai ba'. Wannan shi yasa duk arewacin Nigeria matan wannan garin sunfi kowa bleaching. Kai ba mata kaɗai ba har mazan ma bleaching suke, bazan faɗi suna ba, amma dai ya kamata ku gyara.
Rubutu Masu Alaqa
1. Illolin Maganin Karin Kiba Na Sha Ka Fashe
2. Illolin ciwon koda da yadda mutum zai kare kansa daga kamuwa da ciwon koda
3. Shin Sabawa Da Istimna'i Yana Hana Mace Gamsuwa Yayin Saduwa Da Namiji?
4. Illolin Ciwon Sugar Ga Mace Mai Ciki: Shin Ciwon Sugar Na Hana Haihuwa?
0 Comments