Maganin Laulayin Amai Da Tashin Zuciya Ga Mai Ciki

 

Maganin Laulayin ciki

Matsalar laulayi ko kuma yawan amai da tashin zuciya a watannin ukun farko ga mace mai ciki matsala ce da yawancin mata ke fuskanta. Wannan yanayi wanda a Turance ake kira da kalmar (morning sickness), ba lallai ne ya kasance dole sai da safe ba, yakan iya faruwa a kowanne lokaci na rana. 

Ga wasu mata, wannan al’amarin yana iya zama mai sauÆ™i, yayin da ga wasu kuma zai iya zama matsala mai tsanani da ke shafar rayuwar yau da kullum. Munyi bayanin matsanancin laulayi dallah-dallah a cikin wannan rubutun 'Matsanancin laulayi a farkon samun ciki da kuma yadda ake maganinsa (Hyperemesis gravidarum.'

Akan danganta wannan matsalar laulayi da canje-canjen sinadaran hormones da É—aukar ciki yake kawowa, musamman hormone na hCG wanda ke Æ™aruwa sosai a farkon lokacin É—aukar ciki. 

Tashin zuciya da amai su kan fara ne a makonnin shida zuwa bakwai na ciki, sannan a mafi yawancin lokuta suna raguwa kafin ƙarshen wata na uku. Duk da cewa wannan yanayin galibin magana ba wata matsala ce mai tsanani ba, amma ga wasu mata yana iya kai su ga rashin lafiya mai tsanani da ake kira (hyperemesis gravidarum), matsanancin lailayi, inda su kan samu ƙarancin ruwan jiki da kuma rasa sinadarai masu amfani a jikinsu.

Ga mata masu fama da matsalar yawan laulayi a farkon ciki, rashin iya cin abinci yadda ya kamata yana iya janyo gajiya, rashin Æ™arfin jiki, da kuma faÉ—uwar jini. Wannan yana iya shafar lafiyar uwa da jariri idan ba'a yi saurin kula ba. 

Hanya mafi kyau ta rage wannan matsalar ita ce cin abinci kaÉ—an-kaÉ—an a lokaci bayan lokaci maimakon cin abinci mai yawa lokaci guda. Cin abincin da ke É—auke da carbohydrates, kamar irin su doya, dankali ko biredi, na iya taimakawa wajen rage tashin zuciya. Haka kuma, gujewa abinci ko abubuwan sha masu karfi, musamman waÉ—anda ke da kamshi mai yawa yana iya rage amai da tashin zuciya.

Sannan akwai maganin laulayi ga mai ciki da likitoci ke bayarwa don rage wannan yanayi, amma bai kamata mace mai ciki ta yi amfani da kowanne magani ba tare da umarnin likita ba, domin tabbatar da cewa magungunan ba su cutar da jaririn dake ciki. 

Duk da cewa yawan laulayin amai da tashin zuciya matsala ce da yawancin mata ke iya shawo kanta a gida, yana da matukar muhimmanci mace ta ziyarci asibiti idan yanayinta ya tsananta ko kuma ya hana ta cin abinci gaba ɗaya. Wannan na da mahimmanci domin tabbatar da cewa jaririn dake ciki yana samun duk abincin da yake buƙata don cigaba da rayuwa a cikin ƙoshin lafiya.

Tashin zuciya da amai ba kasafai yake iya zama matsala mai hatsari ba, amma kulawa da jiki da neman taimakon likita idan ya zama dole, na iya sauƙaƙa wannan yanayi da kuma tabbatar da cewa lafiyar uwa da jariri ba za su fuskanci barazana ba. Wannan lokaci ne mai muhimmanci, kuma duk wata kulawa da ake yi tana ƙara tabbacin samun sauƙin haihuwa lafiya.


Rubutu Masu Alaqa

2. Amfani Da Illolin Hanyoyin Tsayar Da Haihuwa Na Har Abada

3. Alamomin Shigar Ciki: Ya Mace Take Gane Tanada Ciki?

Post a Comment

0 Comments