Mene Ne Targaɗe Da Kuma Abubuwan Da Ke Hanawa Targade Warkewa (Ligament Tear)


Targaɗe wani rauni ne dake faruwa ga tantanin da ke riƙe ƙashi da ƙashi a gaɓa. Wannan raunin  kan iya kasancewa sakamakon murɗewa ko ɗamewar gaɓa fiye da ƙima yayin gudanar da ayyukan yau da kullum, wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, da dai sauran su.

Abubuwan da ke hana targaɗe warkewa da sauri

1. Matakin targade: Targaɗe na da matakan tsanani kamar haka:

  1. Matakin farko: Tantanin zai samu rauni saboda ɗamewa ko talewa fiye da ƙima.
  2. Mataki na biyu: Tantanin zai samu rauni saboda 'yar yagewa ko tsagewa.
  3. Mataki na uku: Tantanin zai tsinke gaɓa daya.

Targade

Wannan hoto na nuna tantanan da ke gaɓar idon sawu da tafin sawu ne

2. Warkewa daga raunin targaɗe ya danganta da matakin targaɗe, ma'ana, tsananin raunin da tantanin ya samu.

Tantanin da ke riƙe ƙashi da ƙashi, saɓanin tsoka, ba shi da jijiyar jini kai tsaye da ke kawo masa sinadaran abinci, magani da sauran sinadaran da jini ke ɗauke da su.

Saboda haka, lokacin warkewar raunin tantani kan ɗauki makonni har zuwa watanni gwargwadon tsananin raunin da tantanin ya samu.

Rashin samun kulawar likita da kuma bijire wa ka'idodin da likita ya gindaya, musamman dangane da matakan kariya yayin jinyar raunin, da kuma ƙayyade ranar da ya kamata mutum ya fara taka ƙafar, ko kuma ya koma wasanni.

Domin sau da yawa, 'yan wasa kan koma wasa ba tare da cika makonni ko watannin da likita ya ɗiɓa musu ba. Wanda hakan kan sake ta'azzara raunin kafin ya warke.

© Adopted from Physiotherapy Hausa


Rubutu Masu Alaqa

1. Yadda ake Maganin Ciwon Baya ta Hanyar Motsa Jiki

2. Meke Kawo Ciwon Baya Bayan Aikin Tiyatar Cire Jariri CS

3. Ciwon gwiwa da yadda ake maganinshi (Knee Osteoarthritis)

4. Shin Matsala Ne Dawowar Ruwan Maniyyin Mijina Bayan Mun Gama Saduwa?

Post a Comment

0 Comments