Shawarwari Ga Mata Masu Matsalar Yawan Zubewar Ciki

 

Zubewar ciki

Duk matar da take samun matsalar yawan lalacewar ciki ko zubewar ciki bayan ta samu to akwai buƙatar amfani da waɗannan shawarwarin ko bin waɗannan matakan domin samun mafita.

Wasu matan daga zarar sun samu ciki Yana lalacewa ko ya zube kasa da watanni uku. Dan Haka ga wasu matakan da ya dace ayi amfani dasu da za su iya taimakawa.

1. Daina Shan Magunguna Barkatai

Barin shan duk wani maganin da ba likita ne ya rubuta ba, musamman magunguna masu É—auke da sinadarin caffeine. Matan dake yawan shan magunguna masu É—auke da sanadarin caffeine ko wani abinci mai É—auke shi na daga cikin mahimman abubuwan dake sa ciki ya fita 

Dan haka mata masu É—anyen ciki a kiyaye, ba kowane magani be zaki É—auka ki watsa a cikin ki ba, idan har kina son lafiyar cikin. Duk wani magani da zaki sha ki tabbata likita ne ya rubuta miki, kuma likitan yasan kina É—auke da ciki.

Idan a chan baya kina kan wasu magunguna na rashin lafiya, kamar magungunan ciwon hawan jini ko ciwon sugar, toh daga zarar kin samu ciki, wajibi ne ki garzaya asibiti ji sanar da likitan ki domin bitar magungunan da kike sha.

2. Daina Shan Kayan Maye

Shan kayan maye kamar irin su giya, wiwi da kwayoyin maye suna lalata cikin mace, har ma da shan tabar sigari. Duk da cewa, mutanen mu na hausa fulani mata ba su faye shan tabar sigari ba kamar maza, amma akwai wata baƙar ɗabi'a ta shaye-shayen magungunan maye na syrup da ta zama ruwan dare a cikin 'yan matan wannan zamani.

Shan taba da kuma shaye shayen waɗannan kayan maye ga mace na gaba gaba wajen tabbatar da lalacewar cikin da ta samu. Dan Haka barin wannan ɗabi'ar zai iya samar da abinda ake buƙata.

3. Zuwa Asibiti Domin Bincike 

Ya wajaba ga duk macen da ke samun yawan zubewar ciki taje asibiti domin yin bincike da gano abubuwan da ke kawo mata yawan zubewar cikin. A lokacin da mace taje asibiti za'a yi mata gwaje-gwaje domin tabbatar da lafiyar ta, waÉ—anda suka haÉ—a da screening na infections na mata, PID da sauran wasu cutuka. WaÉ—annan cutuka suna iya jawo yawan barin ciki.

Haka kuma ana iya yiwa mace hoto domin tabbatar da lafiyar mahaifar ta, saboda akwai wasu lalurorin mahaifa da ke iya hana mace riƙe ciki na dogon lokaci. Har wa yau dai, daga cikin gwaje-gwajen da za'a yi a asibiti, akwai awon ciwon sugar (screening test for diabetes). Saboda ciwon sugar yana cikin manyan abubuwan da ke kawo yawan lalacewar ciki, ɓarin ciki da mutuwar yaro a cikin ciki.

Bugu da kari, sauran cutuka masu yaÉ—uwa ta hanyar saduwa suna kan gaba wajen hana mace riÆ™e ciki, ko hana samun shi ma a baki É—aya. Dan haka akwai Æ™alubale ga maigida da uwar gida, mu rage neme neme, musamman magidanta maza, kada kabar uwar gida ka riÆ™a neman mata waje daga Æ™arshe ka kwaso matsala ka kawo gida ya shafi uwargida ya haifar mata da matsalar yawan zubewar. 

Sannan kuma, ga macen da take yawan samun zubewar ciki, akwai buÆ™atar a duba yanayin dukkan sinadaran hormones na jikin ta, saboda matsalar rashin daidaituwar sinadaran hormones (hormonal imbalance) a jinin mace shi ma ba karamin lahani yake yi ba wajen sanya zubewar ciki da ma hana mace daukar ciki baki É—aya.

4. Amfani Da Magungunan Karin Jini

Magungunan ƙarin jini da ake amfani na Folic acid da Fesolate, suna da matuƙar amfani ga mace mai ciki, ana fara amfani da su ne daga zarar mace ta samu ciki, kullum ta sha har sai ta sauka.

Wata majiya mai karfi ta tabbata ana fara shan Folic acid kullum daga zarar mace ta shirya ɗaukar ciki tun kamin ma ta samu, saboda yana da amfani sosai wajen kiyaye haihuwar yara masu naƙasa (Neural tube defects).

Saboda haka, kuyi amfani da Folic acid, lallai akwai ragwada ga duk matar da take samun matsalar yawan zubewar ciki idan tana amfani da wannan karamin magani mai sauƙin kuɗi da kuma sauƙin samu.

Yadda Ake Kula Da Mace Bayan Zubewar Ciki

A lokacin da mace ta samu zubewar ciki akwai abubuwa masu mahimmanci da ya kamata a kula da su domin inganta rayuwar ta da kuma kore mata damuwa da baƙin ciki. Za muyi bayanin su ɗaya bayan ɗaya kamar haka:

1. Ya wajaba a kula da lafiyar ta domin a tabbatar da ba ta samu matsaloli ba sanadiyyar zubewar cikin. Matsalolin da mace zata iya samu  bayan zubewar ciki su ne kamar hakan: 

  • Zubar jini mai yawa
  • Matsanancin ciwon mara
  • ZazzaÉ“i mai tsanani 
  • Fitar ruwa masu wari daga gaban mace
  • Rashin iya É—aukar ciki a nan gaba

2. Ana ba mace magani domin warware matsalolin da take fama da su ko kuma domin kariya daga samun matsalolin. Ana baiwa mace antibiotics da kuma magungunan kashe ciwo.

3. A kula da yanayin abincin mace, ma'ana a ba ta abinci mai gina jiki. Tare da samun isasshen hutu da kuma shan isasshen ruwa da abubuwan kayan lambu da kayan marmari masu ruwa.

4. Akwai buƙatar ita da mijin ta su amince ayi mata family planning na wani ɗan lokaci domin ta samu hutu kuma jikin ta ya murmuje kamin ta sake ɗaukar wani ciki.

5. A kula da lafiyar ƙwaƙwalwarta ta hanyar ba ta magana domin rage damuwan da mace ke shiga bayan ta samu ɓarin ciki.

Kuna iya ajiye tambayoyin ku ta hanyar amfani da akwatin sharhi da ke ƙasa, in shaa Allah zamu amsa.

Post a Comment

0 Comments