Dan Allah Dr. ka amsamin tambaya ta. Mace ce mai cikin sati 6 taje asibiti a kayi mata awon ciki da kuma awon malaria, awon ya nuna duka akwai sai aka ba ta magani har da wannan na malarian mai 4 4 tana cikin sha sai ga jini ya gwacce, har cikin ya zube. To yanzu halin da ake ciki mijinta yace sai ya kai likitan ƙara a kotu, wai ya zubar masa da ciki dan Allah wannan maganin malarian daya bayar yana zubar da ciki ne?
Amsa
Bari mu fahimci abin da ya faru domin a magance wannan matsalar a cikin natsuwa. Maganin malaria mai 4:4 wanda matar ta sha yana cikin dangin magungunan malaria da ake kira da ACT, yana ɗauke ne da sinadaran Artemether 80mg da kuma Lumefantrine 480mg. Ma'ana duk ƙaramar ƙwayar tablet ɗaya tana ɗauke da Artemether 20mg da Lumefantrine 120mg, shi yasa ake shan ƙwayoyin tablet huɗu baki ɗaya domin su bada jimlar Artemether 80/ Lumefantrine 480 wanda shi ne wadataccen maganin da ke yiwa baligi aiki.
Abinda yasa nayi wannan bayani shi ne domin na tabbatar muku da matar ba ta sha maganin fiye da ƙimar da akayi umurni ga manyan mutane ba.
A lokacin ba da maganin malaria ga mace mai ciki ana lura da watannin cikin ta kamin bada magani. Yawancin magungunan malaria da ake bayarwa ga mai ciki, har da Artemether-Lumefantrine (Coartem ko Armatem), basu da wata matsala ga uwa ko jariri idan aka dora mace mai ciki akan su.
Masana sun raba zangon ciki wata tara zuwa gida uku kamar haka:
Zangon farko (First trimester) shi ne a lokacin da ciki yake ƙasa da watanni uku (<3 Months)
Zango na biyu (Second trimester) shi ne a lokacin da cikin ya ke watanni uku zuwa shida (3-6 months)
Zango na uku (Third trimester) shi ne a lokacin ciki wuce watanni shida (>6 months)
Yayin la'akari da waɗannan zangunan rainon ciki hukumar lafiya ta duniya da hukumar lafiya ta Nigeria sun ƙayyade magungunan da ake iya amfani da su wajen maganin malaria ga mata masu ciki. Waɗannan magungunan sune kamar haka;
- Quinine
- ACT wanda ya ƙunshi har da Artemether/Lumefantrine mai 4:4 ɗin da ake magana akai.
Kundin ka'idodin maganin malaria na hukumar lafiya ta Nigeria, wallafar 2011 ya tabbatar da cewa za'a iya amfani da maganin malaria na Quinine a dukkan zangunan rainon ciki (All trimesters) domin magance malaria marar tsanani, saboda bincike ya tabbatar da babu wata illah da wannan maganin zai iya haifar wa ga uwa ko jariri.
Haka kuma wannan kundin ya tabbatar da cewa za'a iya amfani da magungunan ACT a zango na biyu da na uku, saboda bincike ya tabbatar da basu da matsalar komai a waÉ—annan lokuta. Amma a zangon farko na rainon ciki (first trimester) babu isasshen binciken da ya nuna ACT basu da illah, kuma babu binciken da ya nuna suna da illah. Don haka kundin ya bada damar amfani da su a wannan lokaci idan har su kaÉ—ai ne ingantattun maganin malaria da za'a iya samu a wannan lokaci.
Saboda haka zamu iya cewa dalilan zubewar cikin zai iya zamowa É—aya daga cikin waÉ—annan abubuwan:
1. Malaria: Ita kanta cutar Malaria tana cikin manyan abubuwa masu haifar da zubewar ciki, musamman idan ba'a magance ta da wuri ba. Bincike ya tabbatar da cewa a Nigeria tana cikin abubuwan da ke kan gaba wajen kawo zubewar ƙaramin ciki. Don haka ba lallai bane ya zamo cewa maganin ne dalilin zubewar cikin kai-tsaye, saboda cutar Malaria tafi duka magungunan malaria haɗarin zubar da ciki (har da magungunan malaria da aka haramta amfani dasu).
2. Matsalolin na Lafiya: Wani lokaci, ciki yana iya zubewa saboda wasu matsaloli na rashin lafiyar uwa ko jaririnta waɗanda basu da alaƙa da maganin da tasha.
3. Magungunan Malaria: Idan maganin da aka bayar bai dace da mai ciki a watanni uku na farko ba, to, yana iya haifar da matsalolin da zasu iya sanyawa cikin ya zube.
Abin da ya kamata ku yi shi ne komawa asibiti wurin likitan da ya bayar da maganin don a bincika dalilin zubewar cikin. Sannan kai likitan ƙara kotu ba zai zamo mafita ba a gareku, koda kuwa dalilin maganin ne cikin ya zube.
Domin a kowace irin sana'a ko aiki ana samun akasi, bana tsammanin wanda ya bayar da maganin zai yi hakan da ganganci, sai dai bacin rana, bugu da ƙari, mata da yawa suna amfani da wannan maganin a irin wadannan lokutan kuma babu wata matsala .
Sannan idan kuka je kotu, toh aiki fa ya same ku, domin abu ne mai matuƙar wahala ku iya tabbatarwa kotun da cewa maganin malaria ɗin ne yayi sanadiyyar zubewar cikin, tunda ita kanta malaria din tafi maganin haɗarin zubar zubar da ciki.
Kunga a nan, 'yan kudin da ya kamata kuyi cefane, ki ci kaji ki sami lafiyar samun wani ciki zasu kare ne a kotu. Ni dai shawara ta shi ne, ku É—auki kaddara, mijinki yayi amfani da kuddin da zai je kotu ya siyo miki kayan dadi, da zarar kin warke, sai a cigaba daga inda aka tsaya. Fakat.
0 Comments