Mata dayawa na fuskantar wanann al'amari har suna tunanin wani matsala ne, wasu ma ganin suke yi wannan abun shi ne ya hana su daukar ciki, alhali ba wannan al'amari ba matsala ba ne. Mafi yawa matan dai basu daÉ—e da yin aure ba kan samu wanann yanayin na dawowar ruwan maniyyi bayan maigida ya kawo a cikin farjin matar sa.
Binciken kimiyya ya tabbatar da cewa kashi 99.9% na ruwan maniyyin da namiji yake sakewa a cikin farjin mace baya samun shiga cikin mahaifar ta, kashi 0.01% ne kawai ke samun shiga a cikin mahaifa wanda ana tsammanin wannan kashin da ke shiga yana dauke da tantanin halittun haihuwa da sun fi ƙwara 100,000.
A cikin waɗannan tantanin halittun haihuwa dubu ɗari cikin su ƙwara ɗaya ne kawai ake buƙatar ya haɗu da ƙwan mace domin mace ta dauki ciki. Bisa ga dogaro da wannan bincike zamu iya cewa da yaƙini dawowar ruwan maniyyi daga farjin mace yayin fitsari ko kuma lokacin da ta miƙe tsaye bayan gama saduwar aure, ba zai ma rage mata yiwuwar daukar ciki ba balle ma ya hana ta daukar ciki.
Mata dayawa, musamman sabbin amare uwayen zumuɗi suna yawan yin wannan tambayar, wasu ma ganin suke yi kamar sune keda matsala, mahaifar su ba ta iya riƙe ruwan maniyyin namji. Toh wannan ba matsala bane kuma baya hana komai
Da zarar namiji ya kawo a cikin farjin mace, a cikin ƙasa da sa'a ɗaya ƙwayoyin tantanin halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi zasu ruga da sauri suna masu gasa wajen shiga a cikin mahaifa domin haɗuwa da ƙwan da mace ta saki, domin daukar ciki. Saboda haka duk ruwan da za aga ya dawo akwai wanda zai rage mace ta iya daukar ciki dashi matuƙar bakin mahaifar ta ya buɗe.
Wannan shi yasa amfani da hanyoyin bada tazarar iyali na gargajiya wanda ake yi idan namiji yazo kawowa, sai yayi sauri ya zare azzakarin sa ya zubar da ruwan maniyyi a waje, wannan hanya ba ta da tabbas, ba ta hana daukar ciki idan aka dogara da ita kawai.
Dalili kuwa shi ne, akwai ƙwayoyin tantanin halittun haihuwa da kan iya biyo ruwan maziyyi su fito ta azzakarin namiji tun kamin namiji yaji uzurin kawowa, waɗannan ƙwayoyin suna iya yiwa mace ciki koda namiji ya kawo a waje, ma'ana ya zubar da duka ruwan maniyyin sa a waje. Haka kuma, idan namiji bai yi saurin zarewa ba, zubar ruwan maniyyinsa kimanin rabin ɗigo a cikin farjin mace, zai iya yiwa mace daukar ciki ko da ya zubar da galibin ruwan maniyyinsa a waje.
So a ƙarshe zan rufe da cewa gaskiya lafiya lau ne, babu matsala dan mace taga irin hakan a tare da ita, a daina damuwa ana kashe kuɗaɗe wajen masu maganin gargajiya, saboda wannan baya hana ko rage yiyuwar daukar ciki.
0 Comments