Shin Rashin Aure Yana Sa Gaban Mace Budurwa Ya Buɗe Bayan Wasu Shekaru?

Meke kawo budewar gaban mace


Dr wai Dan Allah da gsky ne idan macce ta kai shekara 27 ko 28 batayi aure ba zata iya budewa. Takoma kamar wacce tayi aure?


Amsa

Ba abin da ke sa gaban mace ya bude mace ta zama kamar wadda tayi aure sai saduwa da namiji ko kuma idan tana amfani da wasu abubuwa a gabanta domin biyawa kanta buƙata da kanta. 

Akwai abinda ake cewa tantanin budurci, wanda aka fi sani da hymen a turance, wani ɗan tsoka ne mai raga wanda ya rufe kofar farjin mace budurwa wadda bata taɓa saduwa ba, kuma bata yin wasa da gabanta domin biyawa kai bukata.

Duk da cewa wannan tsokar takan iya fashewa ko da mace bata taɓa yin aure ba, wasu mata ma nasu yakan fashe tun kamin su balaga saboda yawan tsalle-tsalle, tsallaken gota ko wani haɗari da kan iya tale ƙafafun mace da ƙarfi. 

Amma fashewar wannan tantanin ta wata hanya ba ta saduwa ba bata sa gaban mace ya buɗe. Sai dai a lokacin da zatayi saduwa a daren farko ba lallai ne ta samu zubar jini ba.

Karanta Rubutu Masu Alaqa 

1. Budewar Gaban Mace Da Kuma Yadda Yake Samun Kari Yayin Haihuwa

2. Bushewar Gaban Mace, Rashin Ni'ima Da Kuma Kankancewar Gaba

3. Maganin Matsi Na Asibiti: Tiyatar Tsukewar Gaban Mace

4. Maganin Kaikayin Gaba Na Budurwa: Meke Kawo Kaikayin Gaba Na Mata

Post a Comment

0 Comments