Dr. Inada wata damuwa ne bansan kokasan mafita ba, mace ce tanada sha'awa kuma tana jin daɗin wasa (romance) sai dai kuma bata Jin dadin saduwa da mijinta. Kome mijin zai yi mata bata taɓa jindaɗin wani abu daya shafi saduwar su.
Sai dai tana aikata istimna'i (masturbation), idan tana yi ba ta saka hannunta a ciki sai a kan clitoris dinta take gamsuwa. Dan Allah idan baka sani ba ka bincika mun.
Amsa
Alƙalumman bincike sun nuna cewa, rashin gamsuwa ga mace yayin saduwa da namiji, raguwar ni'imar gaban mace, jin zafi yayin fitsari, jin zafi yayin saduwa, duka suna daga cikin matsalolin da yin istimna'i ke kawowa ɗiya mace.
Matuƙar akwai sha'awa tare dake, to tabbas idan baki samun gamsuwa a wajen saduwa da mijin ki, toh baki samun isasshen gogayya ne daga al'aurar mijinki irin gogayyar da zata baki gamsuwar da kike buƙatar.
Wannan yakan iya samo asali ne daga sabawar da kika yi da yin wasa da gabanki da saka hannu clitoris dinki domin samarwa kanki gamsuwa. Yawan yin haka ya sanya jikin ki ya saba idan ba'a taɓa gabanki irin yadda kike yi ba a lokacin istimna'i toh ba zaki samu gamsuwa ba. Shi kuma azzakarin mijinki ba ya iya shafa clitoris dinki kamar yadda kika saba shafawa da hannunki.
Bugu da kari, clitoris dinki yafi cikin farjinki jin taɓi, motsa sha'awar 'ya mace da kuma samar da gamsuwa. A yayin da kika saba da samun gamsuwa ta hanyar wasa da clitoris dinki, ba zaki ji wani daɗi na musamman ba yayin da namiji ke saduwa dakebta farjinki ba. Kamar mutum ya saba da shan zuma ne, sai a ɗanɗana masa ɗigon ruwa a baki. Akwai matan da aka ruwaito cewa su gaba ɗaya basa samun gamsuwar jima'i dole sai anyi musu wasa da wannan beli (clitoris) na su.
Haka kuma, damuwa irin wannan tana iya zama abu mai wahala ga mace, amma yana da mahimmanci a fahimci cewa yana iya zama wani abu mai alaƙa da yanayin jikin ta ko kuma yanayin ƙwaƙwalwar ta (psychological problem). Ga wasu abubuwan da zasu iya kawo irin wannan matsalar.
1. Matsalolin Lafiya:
Hormonal imbalance: Rashin daidaituwar sinadaran hormones a cikin jinin mace kamar estrogen da testosterone na iya shafar sha'awa ko jin dadin jima'i.
Vaginal infections ko cututtuka na gaban mace: Wasu cututtuka na iya hana jin dadin sex, kamar vaginitis, endometriosis, ko kuma matsaloli da suka shafi pelvis.
Yanayin jin daÉ—in mace: Wasu matan suna jin daÉ—i ne kawai ta hanyar clitoris, ba ta hanyar sex mai zurfi ba, kuma wannan ba matsala ba ce a gaskiya.
2. Matsalolin Ƙwaƙwalwa:
Stress ko damuwa: Idan kina cikin damuwa ko matsalolin rayuwa, wannan yana iya rage jin dadin saduwar aure.
Samun rauni a baya: Idan kin taɓa fuskantar wani abu da ya cutar da ke ta fuskar saduwa, wannan yana iya haifar da rashin jin daɗin sex.
Damuwa game da yadda zaki samu gamsuwa: Idan kina jin tsoron rashin jindaÉ—i ko rashin gamsuwa, wannan kansa na iya hana jindaÉ—in saduwa.
Mene ne Mafita?
1. Nemi likitan mata (Gynecologist): Zai taimaka miki wajen duba lafiyar jikin ki kuma ya tabbatar da babu wata matsala ta lafiya tare da ke.
2. Nemi likitan ƙwaƙwalwa (Behavioural therapist): Idan damuwar ki tana da alaka da psychological issues, likita zai taimaka wajen gano matsalar da baki shawarwarin da suka dace da ke
3. Tattaunawa da mijinki: Yana da kyau ku tattauna da mijinki tare da fahimtar juna. Ko zai yiwu ya canza salon yadda yake saduwa dake, kuma yayi miki duk abubuwan da kike buƙata yayin saduwa, hakan zai taimaka miki sosai.
4. Koyi hanyoyi daban-daban: Maimakon masturbation ta hanyar beli (clitoris) kawai, ki koyi hanyoyin daban daban yadda ake saduwa mace da namiji, kiyi kokarin gwada hanyoyin tare da mijinki domin jikin ki ya saba.
5. Gudun damuwa da yawan motsa jiki: Yin motsa jiki, hutawa, da rage damuwa na iya taimakawa sosai wajen jindadin saduwar aure.
0 Comments