Yadda Ake Kamuwa Da Cutar HIV Ta Hanyar Saduwa: Shin Ana Iya Kamuwa Bayan Amfani Da Baki?

HIV and sucking


Assalamu alaikum, ni tambayata anan shin sai namiji yayi releasing a cikin mace kekamuwa da cutar h. I. V kokuwa ranar farko dasuka fara Muamula ta jimai zata iya kamuwa ko akasin Hakan , shinkuma zata iya dauka tahanyar idan ya Yi socking dinta da harshe shin insunyi abin kamar da kwana biyu ko ukku taji tana zargin kamar yanada kwayar cutan akwai wata hanya dazatabi Dan kariya kan cutar ta yadu ajikinta

Amsa

Ba sai namiji yayi releasing a cikin mace sannan zata iya kamuwa da cutar HIV ta hanyar saduwa ba, idan dai har ya sadu da ita, daga zarar ya sanya azzakari a cikin farji toh akwai yiwuwar yaÉ—uwar wannan cutar, saboda haka mace za ta iya kamuwa da cutar HIV idan har namiji yana da cutar, haka ma namiji zai iya kamuwa idan mace tana da cutar.

Amma idan bai sanya azzakari a cikin farji ba, kawai yayi sucking din gaban mace ne da harshen sa ko dukkan bakin sa, toh akwai Æ™arancin yiwuwar yaduwar wannan cutar ta HIV, amma duk da haka shi da ya sanya bakin sa a gaban mace yana kan hatsarin kamuwa da cutar HIV idan har mace tana dauke da cutar. 

Cutar HIV ta Hanyar sucking

A irin wannan saduwar ta (oral sex) wanda ke amfani da bakinsa yafi kan haÉ—arin kamuwa da cutar fiye da wanda ake tsotsa idan har abokin saduwar sa na É—auke da cutar. Haka ita ma mace idan tana tsotse namiji toh akwai yiwuwar yaÉ—uwar wannan cutar, amma mace tafi zama kan haÉ—arin kamuwa, saboda tana amfani da bakin ta shi kuma yana amfani da azzakarin sa.

Dalili kuwa shi ne kwayoyin cutar HIV sun fi yawa a cikin ruwan da ke fita daga gaban mace ko azzakarin namiji a yayin saduwa, ba suda yawa a cikin yawun baki. Haka kuma gaban mace da azzakarin namiji sun fi saurin daukar cutar HIV fiye da baki.

Idan har mace ta sadu da namiji daga baya tayi zargin yana dauke da wannan cutar ta HIV, babban abinda ya dace shi ne ta fara tabbatar da cewa yana dauke da cutar kamin ta fara neman hanyoyin kariya. Idan har ta tabbatar da yana dauke da cutar HIV a cikin kwanaki uku bayan sun gama saduwa, toh akwai magungunan da ake iya bata domin kare ta daga kamuwa da wannan cutar, ana kiran wadannan magungunan da post exposure prophylaxis (PEP).

A lura cewa, dole sai an tabbatar da wanda aka sadu dashi yana dauke da cutar kamin a fara shan wadannan magungunan. Haka kuma, magungunan ba su da tabbaci É—ari bisa É—ari da zasu kare mutum daga kamuwa da cutar HIV ko da ya fara su a cikin lokaci, sannan dole ne a fara su cikin kwanaki uku bayan saduwa da mai cutar, the earlier the better, idan ya wuce kwanaki uku ba'a fara ba, toh farawa bashi da wani amfani.

Post a Comment

0 Comments