Yadda ake Maganin Ciwon Baya ta Hanyar Motsa Jiki


Sau da yawa idan mutum ya ce "ina fama da ciwon baya", sai ka ji wani ya ce "ba ka motsa jiki ne", ko kuma ya ce "ka riÆ™a motsa jiki akai-akai". To amma abin tambaya a nan shi ne: wane irin motsa jiki ne ke taimaka wa mai ciwon baya? 

Da farko dai, ya kamata mu bambance tsakanin "motsa jiki" da kuma "atisaye".

Motsa jiki yana nufin duk wani yunƙuri da ya haifar da motsin jiki ko gaɓoɓi saɓanin hutu. Wato hutu shi ne lokacin da mutum ke kwance ko zaune ba tare da yana yin wani aiki ba. Misalan motsa jiki sun haɗa da: ayyukan gida, aikin gona/lambu, tafiya, sassarfa, gudu, tsallake-tsallake, tuƙa keke da sauran ayyukan yau da kullum.

Amma shi kuwa atisaye, kalma ce wadda Bahaushe ya aro daga turanci, wato "exercise", sannan ya yi mata kwaskwarima zuwa "atisaye". Atisaye na nufin tsararre, aunanne, ƙayyadajje, kuma keɓaɓɓen motsa jiki domin magance wata matsala ko bunƙasa aikin wani sashin jiki ko gaɓa ko kuma bunƙasa dukkanin jiki baki ɗaya.

Saboda haka, kamar yadda nau'o'in ƙwayar magani ke da yawa, kuma kowacce ƙwaya ke da keɓaɓɓen aiki domin ciwuka daban-daban, haka ma atisaye ke da nau'o'i daban daban domin ciwukan jiki ko gaɓoɓi daban-daban. Har ila yau, nau'in atisayen mai ciwon gwiwa ba zai zama iri ɗaya da na mai ciwon baya ko mai ciwon wuya ba.

Bugu da ƙari, shi kansa ciwon bayan yana da sabuba daban-daban. Wani ciwon bayan yana faruwa ne sakamakon tsinkewar nama, targaɗe, fashewa, bulli ko zaizayewar faifan tsakankanin ƙasusuwan gadon baya, shaƙewar jijiyar laka a gadon baya, gocewa ko karayar ƙashin gadon baya da dai sauransu. To yanzu mene ne sababin ciwon bayan ka?


Saboda haka, kamar yadda abubuwan da ke kawo ciwon baya suka sha bamban, tilas shi mal ma nau'o'in atisayen da zai magance nau'o'in ciwon bayan su bambanta.

Abu mafi ban tsoro akan kasadar fara motsa jiki ko atisaye ga masu ciwon baya ba tare da tuntuɓar likitan fisiyo ba shi ne; sau da yawa, wasu ire-iren motsa jiki ko atisayen da mutane ke yi sune ke ƙara ta'azzara ciwon bayan. Ko kuma a shafe tsawon lokaci ana yi amma babu wani jin sauƙi, ko ciwon bayan ma ya ƙaru.

Daga ƙarshe, ya zama wajibi ga duk mai wani nau'in jiki, ciwon baya, ciwon wuya, ciwon ƙafaɗa, ko ciwon gaɓɓai da ya guji fara yin duk wani irin motsa jiki ko atisaye da nufin magance wani ciwo ba tare da tuntuɓar likitan fisiyo ba.

Saboda kafin a samar da wani nau'in motsa jiki ko atisaye ga mai wani nau'in ciwon baya, sai an nazarci abubuwan da suka kawo masa ciwon, sannan a ɗora mutum a kan ƙeɓaɓɓen atisaye da shawarwarin da za su taimaka wajen sauƙaƙa ko magance ciwon bayan.

Bugu da ƙari, akwai kayan aiki da nau'rori na musamman da likitocin fisiyo ke amfani da su wajen rage raɗaɗin ciwon baya. Wannan hanya ce da ake magance ciwo ba tare da dogaro da shan ƙwayar maganin rage ciwo kullum ba.

Don haka, yin atisaye ko motsa jiki ga mai ciwon baya, ciwon gwiwa, ciwon gaɓɓai da dai sauransu, da nufin warkar da ciwon ba tare da tuntuɓar likitan fisiyo ba tamkar shan magani ne ba tare da tuntuɓar likita ba.

Adopted from Physiotherapy Hausa


Rubutu Masu Alaqa 

1. Shin Sabawa Da Istimna'i Yana Hana Mace Gamsuwa Yayin Saduwa Da Namiji?

2. Yadda Ake Kamuwa Da Cutar HIV Ta Hanyar Saduwa: Shin Ana Iya Kamuwa Bayan Amfani Da Baki?

3. Mene Ne TargaÉ—e Da Kuma Abubuwan Da Ke Hanawa Targade Warkewa (Ligament Tear)

4. Shin Matsala Ne Dawowar Ruwan Maniyyin Mijina Bayan Mun Gama Saduwa?

Post a Comment

0 Comments