Yadda ake maganin taibar tumbi bayan haihuwa

Maganin tumbi bayan haihuwa


Tumbi ko taiɓar ciki na daga cikin sauya-sauyen goyon ciki da ke wanzuwa bayan haihuwa. Kuma abu ne da ke munana sifar jikin mace, sanya damuwa, a wasu lokutan ma har da fuskantar tsangwama daga mazaje.

Meke kawo taibar ciki bayan haihuwa?

Daga cikin sauya-sauyen da mace ke samu a lokacin da take ɗauke da ciki akwai ƙaruwar taruwar kitse a sassan jikinta har da cikin ciki.

Har wa yau, sinadaran hormones na haihuwa suna sanya tsokoki da tantanan jiki su yi laushi sosai domin shirya jiki da al'amarin haihuwa. Bugu da ƙari, nauyin jariri da nauyin mahaifa da suke jingine a kan tsokoki da tantanin ciki suna ƙara janyo talewar tsokoki, tantanin ciki da fatar ciki. Waɗannan dalilai su ne ke janyo tumbi ko teɓar ciki bayan haihuwa.

A lura cewa, mafi akasarin lokuta, wannan taiɓar ciki da ke faruwa bayan haihuwa baya da alaƙa da girman mahaifa. Dalili kuwa shi ne, bincike ya tabbatar da cewa mahaifa takan zuƙe bayan haihuwa ta koma asalin girman ta kamin daukar ciki, a cikin lokacin da bai wuce makonni shida bayan haihuwa ba.

Yadda ake maganin taibar tumbi bayan haihuwa 

Duk da cewa abu ne gama-gari ga uwaye bayan haihuwa, to amma yana sanya wasu mata cikin rashin jin daÉ—i ko damuwa, musamman waÉ—anda ke yawan damuwa da kyawun halittar su.

Sai dai, babu buƙatar shiga damuwa ko baƙin ciki musamman ga abun da ake iya magance shi ta hanyar tsara chimaka da kuma keɓaɓɓen atisaye na musamman.

Sau da yawa, uwaye suna ƙin yin ƙorafin teɓar ciki bayan haihuwa saboda kunya ko kuma fargabar cewa likitoci maza ne za su gan su. To albishirinku, domin akwai ɓangaren fisiyo da ke kula da matsalolin mata khususan kuma kina da damar zaɓar mace ƴar uwarki domin ta duba ki.

A cikin wannan hoton vedion zamu ga cewa wata mata tana amfani da itace da sunan hanyar rage tumbi, wannan ba hanyar kwarai ba ce. Toh amma daga baya akwai wasu mutane uku suna koya wasu daga cikin atisaye na musamman domin rage taiɓar ciki.

A lura cewa, waÉ—annan atisaye ba su kaÉ—ai ne atisayen rage tumbi ba, kuma kwaikwayon su kadai baya wadatar wa da ganin likitan fisiyo. Domin magance teÉ“ar ciki bayan haihuwa, tuntuÉ“i likitan fisiyo a yau. 

© Physiotherapy Hausa

Post a Comment

0 Comments