Cervical cancer cutar kansa ce ko ciwon daji ne da yake shafar sashen mahaifa da ke buÉ—ewa a lokacin haihuwa wanda ake kira da cervix a turance ko kuma bakin mahaifa da Hausa.
Meke Kawo Ciwon Kansar Bakin Mahaifa?
Har ila wa yau, ba'a san takamaiman abin da ke kawo wannan cutar kansa ba, amma akwai abubuwa dayawa da kan É—ora mace kan haÉ—arin kamuwa da cutar kansar bakin mahaifa kamar haka;
1. Kamuwa da cutar virus na Human Papilloma Virus (HPV).
Wannan shi ne babban cutar da ake alaƙantawa da cutar cervical cancer, mafi yawancin masu cutar cervical cancer sun fara kamuwa da wannan cutar ne ta rikiɗa ta kawo musu wannan cutar ta kansar bakin mahaifa. Ana kamuwa da wannan cutar HPV ne ta hanyar saduwa tsakanin mace da namiji. Yana da kyau a lura cewa, amfani da robar kariya ta kondom a lokacin saduwa ba ya hana yaɗuwar wannan cutar ta HPV.
Haka kuma yana da wahala a tantance namiji me ɗauke da wannan cutar ta HPV saboda bata kawo musu wani babban damuwa, ko nuna wasu alamomi na takamaiman, alamar da kawai take nunawa ga maza shi ne, takan iya kawo musu ƙuraje ƙanana a gabansu, ko a jikin azzakari ko a fatar ya'yan maraina.
Amma ga mata, cutar HPV takan kawo musu kurajen gaba (Genital warts) wanda daga baya sai cutar ta shafi bakin mahaifa ta kawowa mace cutar kansar bakin mahaifa. Ko ga maza ko ga mata, kurajen HPV basuda ciwo, amma watarana sukan iya zuwa da ƙaiƙaiyi sosai, mutum ya fara jin kaikayin gaba.
Haka kuma, kurajen cutar HPV basujin magani, idan kaga mace ko namiji na fama da kurajen gaba da har na tsawon watanni ko shekaru yana neman magani, amma sunƙi ɓacewa, kila ma sai ƙara girma suke, toh akwai yiwuwar kurajen cutar HPV ne.
2. Gado
Idan cikin dangin mace makusanta kamar uwa ko yaya ko ƙanwa ta kamu da wannan cutar kansar bakin mahaifa (cervical cancer), toh hakan ma yana saka mace akan hatsarin kamuwa da cutar.
3. Saurin Fara Saduwa
Aure ko Kuma fara saduwa a lokacin da mace ke da ƙananan shekaru sosai shima yana cikin abinda masana ke ganin yana sanya mace kan hatsarin kamuwa da cutar kansar bakin mahaifa.
4. Hanyar Saduwa
Saduwa da mazaje barkatai ko kuma karuwanci ko matar da mijinta ke neman mata barkatai (high risk partner) duk waÉ—annan suna É—ora mace kan haÉ—arin kamuwa da cutar HPV da zata kawo mata cutar kansar bakin mahaifa.
5. Raunin Garkuwar Jiki
Mata masu tsananin raunin garkuwar jiki, kamar irin masu cutar HIV wadda har ta kai ga matsayin AIDS suna iya samun cututtukan kansa da dama. Cutar kansar mahaifa da kuma kansar fata da ake kira Karposi Sarcoma na daga cikin manyan cututtukan kansar da suke samu. Wani bincike ya tabbatar da cewa mata masu cutar HIV sun ninka sauran mata hatsarin kamuwa da cutar cervical cancer har sau biyar.
6. Yawan Haihuwa
Waɗannan sune manyan abubuwan da ke ɗora mace kan hatsarin kamuwa da cutar kansar bakin mahaifa, amma akwai wasu ƙanana da masana suka ayyana kamar haka:
- Macen da ta fara al'ada tana da kananan shekaru sosai
- Macen da ta tsufa ta daÉ—e bata daina yin al'ada ba.
- Shan taba ko barasa
- Shan kwayoyin tazarar haihuwa
- Da dai sauransu.
Alamomin Cutar Kansar Bakin Mahaifa
- Ramewa ba gaira ba dalili
- Jin zafi sosai a mahaifa yayin saduwa
- Ganin jini bayan gama saduwa
- Fitar jini mai wari haÉ—e da majina a gaban mace
- Rikicewar jini al'ada
- Ciwon baya da yaki chi yaki cinyewa
Hanyoyin Kariya Daga Cutar Kansar Bakin Mahaifa
Matakin farko na kariya daga wannan cutar shi ne faÉ—akarwa da kuma sanin abubuwan da ke sanya mace kan hatsarin kamuwa da wannan cutar kansar bakin mahaifa da kuma kame kai da kiyaye waÉ—annan abubuwan. Munyi bayanin waÉ—annan abubuwan a sama, saboda haka dole ne mutum ya kiyaye bakin gwargwado.
Mataki na biyu shi ne, akwai gwajin bakin mahaifa da ake yiwa mata wanda ake kira da gwajin pap smear (pap smear test) a turance. Wannan gwajin yakan duba tantanin halittun bakin mahaifa, ya ga ko sun fara samun canje-canjen komawa irin na cutar kansa, ko kuma sun fara samun irin canje-canjen da cutar HPV take haddasawa bakin mahaifa kamin ta zama cutar kansa.
Ana son duk wata mace da tayi aure ko take saduwa da namiji da tayi wannan gwajin a ƙalla sau ɗaya a kowace shekara. Wannan zai bada damar gane cutar kansar bakin mahaifa da wuri, tun kamin ta fara nuna alamomin komai. Mun riga mun karanta a baya cewa, idan cutar kansar bakin mahaifa ta fara nuna alama to ta riga ta bunƙasa.
Domin kariya daga kamuwa daga cutar cervical cancer ko kuma kansar bakin mahaifa an kirkiro alluran riga-kafi ta cutar HPV. Wannan alluran riga-kafi ana yiwa kowace mace daga yarinya yar shekara 9 zuwa sama, anaso kowace mace ta samu wannan alluran riga-kafi ba kawai sai macen da ke kan hatsarin kamuwa da cutar ba. Ko mace tayi aure ko ba tayi ba, ko tanada namiji ko batada ana so kowace mace ta tabbata tayi wannan alluran domin samun kariya daga wannan cutar HPV mai kawo kansar bakin mahaifa.
Kammalawa
Rubutu Masu Alaqa
1. Jin Zafi Yayin Saduwa: Abubuwan da Ke Kawowa da Kuma Yadda Ake Maganin sa
3. Wayar da kan jama'a akan alamomin ciwon daji/kansar kwan haihuwa na mata (Ovarian Cancer Awareness)