Fitar farin ruwa a gaban mace: Wane ne da matsala wane ne ba matsala?


Mafi yawancin mata suna samun fitowar farin ruwa daga gaban su a duk lokacin da suke yin jinin haila. Aƙalla mata dayawa suna ganin farin ruwa mai kauri ko salala, mara launi yana fito musu a kowace rana, adadin da ya kai kimanin da zai iya cika chokalin shayi (tea spoon). Launin ruwan yana iya sauyawa daga farin madara, zuwa farin ruwa, ko kuma baƙi-baƙi (brown) idan suna daf da ganin jinin haila ko bayan gama jinin al'ada.

Bambancin launin ruwan ko kaurin sa yana da alaƙa ne da canje-canjen sinadaran hormones (hormonal changes) a jinin mace a lokacin da yake fitowa. Wadannan sinadaran hormones na mata kamar irin su progesterone da oestrogen, sauyin yanayinsu ne a jinin mace ke sa tana ganin ruwan niima (normal vaginal discharge) na fito mata akai-akai, kuma wannan shi ke sanya gaban ko wace mace baliga ya zamo cikin halin danshi a kowane lokaci.

Fitar farin ruwa a gaban mace wanda keda alaÆ™a da jinin haila 

Fitar farin ruwa daga gaban mace

Wannan fitar farin ruwa da mace take gani daga gabanta kafin period dinta ko bayan gama period ba matsala bane, babu matsala tattare da hakan. Abu ne na yau da kullum da ake kira "Leukorrhea". Wani lokacin ruwan yana iya kasance wa yellowish.

Fitar farin ruwa mai kauri kamar madara-madara haka da yake zuwa kamin fara jinin haila yana faruwa ne saboda yawan sinadarin hormone na progesterone dayake taruwa a jinin mace. A wannan lokacin ana kiran yanayin da "luteal phase". Idan kuma sinadarin estrogen ne yayi yawa a jinin mace toh a lokacin, sai ruwan ya kasance fari-fari, mai yauƙi ko kuma ruwa-ruwa.

Koma ya launin ruwan ya kasance, fari ne, ruwa-ruwa ne, madara-madara ne, yana da kauri ko akasin haka, muddin baya wari ko qarni, gaban mace baya zafi, kaikayi ko raÉ—aÉ—i, toh wannan normal ne, ba matsala bane.

Aikin wannan ruwan shi ne yayi wanke duk wani datti daga gaban mace, duk wasu miyagun kwayoyin cuta da kuma sanya gaban mace zama a cikin halin danshi a kowane lokaci. Hakan yana nuna alamar mace baliga kuma mai lafiya.

Idan mace taga wani irin ruwa mai kalar  anta-anta (brown discharge) bayan ta gama period É—inta ko kuma, bayan jinin hailarta ya É—auke, sai ta sake ganin wani ruwa baÆ™i-baÆ™i haka brown ya zo mata, toh shi É—in wannan ruwan yana kasancewa tsohon jini ne da ya dasÆ™are bai samu daman fitowa ba a lokacin da take yin hailarta. Shi ne yanzu yake fitowa.

Idan kuma brown discharge É—in kafin ma ta fara period ne fa? Ko kuma taga jinin É—an kaÉ—an ya fito ba yadda ta saba gani ba a lokacin da take tsammanin period dinta? Shi kuma yana iya kasancewa alama ce ta "implantation" daga farko farkon samun ciki. Maza kiyi kokari kije pregnancy test domin a tabbatar da hakan ko akasin hakan. Zaki iya yin gwajin ciki a gida na fitsari da tsinke.

Fitar farin ruwa a gaban mace lokacin ovulation 

Yawanci mata suna samun bushewar gaba kamar na kwana 3 zuwa 4 a kowane lokaci bayan yankewar period ɗinsu. Bayan wadannan kwanakin, farin ruwa mai danƙo yakan sake ɓullowa mace wanda zai yi kamar kwana 4 zuwa 5 kafin lokacin ovulation ɗinta, wannan alama ce da ke nuna eggs ɗinta sun fara girma. Ana kiran wannan lokaci da "follicular phase" wanda ke nuna cewa a lokacin ne ƙwan da take saki a lokacin ovulation ke kokarin girma.

Idan kuma lokacin ovulation yayi, ruwan sai ya chanja daga mai danƙo zuwa fari mai yauƙi da santsi kuma mara kauri (salala) haka. A wannan lokacin yana ƙara yawa sosai fiye da na kullum. Shi kuma irin wannan ruwan ana kiran shi "egg white", ganin irin wannan ruwan yana ɗaya daga cikin manyan alamomin ovulation.

Aikin wannan ruwan mai santsi da ke fitowa a lokacin ovulation shi ne ya taimaka wajen sanya santsi a gaban mace da kuma bakin mahaifa (cervix) ta yadda ya'yan halittun ruwan maniyyi zasu iya shiga a cikin mahaifa da gudu don cimma Æ™wan da mace ta samar domin samun ciki. 

Sannan mata dayawa suna amfani da ganin irin wannan farin ruwan a matsayin babbar alama ta ovulation ɗinsu, hakan yana taimaka musu wajen planning kwanciya da mazajensu domin samun ciki da wuri ko kuma ƙauracewa yin saduwa a wannan lokacin idan basu buƙatar samun ciki. Wannan tsarin shi ake kira da "natural family planning" ko "fertility awareness method".

Ana kiran tsarin da natural family planning idan har mace tayi amfani da wannan hanyar ta kauracewa mijinta domin hana samun ciki. Ana kiran sa fertility awareness method idan har mace tayi amfani da wannan tsarin ta ƙara ƙaimi wajen saduwa da mijinta domin ta samu ciki.

Wannan ruwan da ke fita a lokacin ovulation yana fara fitowa ne ruwa-ruwa mai  yauÆ™i da santsi sosai a farkon yin ovulation (cikin kwanaki biyu da yin ovulation), a wannan lokacin ne Æ™wan yake zaman jiran mace ta sadu da namiji domin ya haÉ—u da tantanin halittun ruwan maniyyi. Amma daga baya, kamar kwanaki (3) bayan ovulation ruwan yakan yi kauri, ya rage santsi. Wannan na nuni da cewa Æ™wan ya gaji da jiran maniyyi ya mutu, saboda haka a wannan lokacin ko mace ta samu saduwa ba zata iya É—aukar ciki ba.

Toh irin wannan ruwan  mai kauri mace za ta cigaba da gani daga bayan ovulation har zuwa wani period din. Daga bayan ovulation din zuwa wani period, yawan fitowar ruwan zai dinga raguwa a hankali, yana zamowa mai kauri kuma mai danÆ™o, wani lokaci har mace za ta iya jinsa kamar wana gam ko glue.

A matsakaici dai yana iya kaiwa irin kwana 11 zuwa 14 tsakanin ovulation É—inki zuwa wani period dinki kenan. Wasu lokuta kina iya ganin fitar wannan ruwan yellowish haka kafin period dinki.

Meke kawo fitar ruwa daga gaban mace 

Akwai abubuwa dayawa da ke iya kawo fitar ruwa daga gaban mace da zamu kasa gida biyu kamar haka:

1. Normal Vaginal Discharge: WaÉ—annan sune ke kawo fitar ruwa a gaban mace wanda bayada matsala. Ruwan lafiya ne, niima da kuma sauye-sauyen sinadaran hormones a jinin mace. Ga ire-iren fitar ruwa a gaban mace da baya da matsalar komai;

  • Ruwan niima da ke fitowa mai wanke dattin gaban mace, sanya gaban mace a cikin danshi da kuma nuna cikar lafiyar 'ya mace. Irin wannan ruwan na iya zamowa mai kauri ko mara kauri, mai yauÆ™i  kuma mai santsi. Sannan baya wari ko Æ™arni. Wasu suna kiran shi da "egg white mucus"
  • Normal side effects na family planning; Sakamon sauyin yanayin levels na sinadaran hormones da amfani da family planning ke kawowa, hakan yana sa fitar ruwa a gaban mace ya Æ™aru.
  • Pregnancy: Wani lokaci yawan fitar farin ruwa a gaban mace kafin lokacin normal period yazo yana iya zama alama ce ta É—aukar ciki. Musamman ma idan mucus din ya kasance mai kauri kuma ruwan madara-madara.

2. Abnormal Vaginal Discharge: Wannan kuma shi ne fitar ruwa a gaban mace wanda wasu kwayoyin cuta ke kawowa. Akwai abubuwa da dama da ke iya kawo wannan, amma ga wasu daga cikin su;

  • STIs (Sexually Transmitted Infections): Cututtukan da ke yaÉ—uwa ta hanyar saduwa kamar su Gonorrhoea, Chlamydia, Trichomonas duk suna jawo mace tayi ta ganin fitar ruwa ta gaban ta. Gonorrhoea da Chlamydia su yawanci ba sa ma nuna wata alama da tafi wannan ruwan, sannan discharge É—insu yana nan ne mai kauri ne, mai dimbin yawa da wari.
  • Ita kuma cutar Trichomonas; fitar ruwan da take kawowa yana fitowa ne yellow ko kore haka, sannan yana Æ™arnin kifi-kifi, kuma ga kaikayin gaba na tsiya.
  • Candidiasis (yeast infection): shi kuma discharge dinsa fari ne mai kauri, kamar farin madara. Shi ne wani lokaci zaku ga yana fitowa kamar dussa-dussa haka. Yana zuwa da wasu alamomi kamar kaikayin gaba da jin zafi a gaban mace (ta ciki da ta wajen).
  • Bacterial Vaginosis: Ita ma wata cuta ce da ke kawo fitar ruwa a gaban mace mai kama da toka-toka (gray-white) sannan yana sa warin gaba kamar Æ™arnin kifi kifi haka.

Kammalawa 

Duk lokacin da kika ga ruwa yana fitowa ta gaban ki, kana fari ne, madara-madara ne, mai kauri ne ko salala ne, mai yauki ne ko mai santsi ne, muddin baya wari kuma baya zuwa da kaikayin gaba kuma baya zuwa da raÉ—aÉ—i ko jin zafin gaba ko kuma jin zafi yayin fitsari ko jin zafi yayin saduwa da miji, kawai salun ahlun yake fitowa abin sa, toh kar ki tada hankali wannan ba matsala bane. Alama ce na jikin ki a matsayin ki na 'ya mace yana aiki yadda yakamata kuma kina a cikin koshin lafiya.

Idan kuma kinga ruwa yana fito miki ko ma ya launin sa yake, kuma sai tare da hakan akwai zafin gaba, kaikayin gaba, ko warin gaba, kumburin gaba, kurajen gaba ko É—aÉ—ewar fatar shi, ta ciki ko ta wajensa, ko kuma duka biyun, to maza maza kiyi saurin zuwa asibiti domin magani.