Assalamu Alaikum doctor barda yau da kuma kokari. Don Allah doctor mace Mai ciki tsawon watanni uku kenn tana fama da Amai Mai tsanani kuma Bata tashin zuciya kamar Tara yawu a Baki sai dai kawai Aman neh yake tokareta A kirji idan batayi ba sai numfashin yayi ta sama sama idan tazoyin Aman kuma sai tayi ta kakari kamar bazata daina ba shiyasa idan tayi Aman jikinta har rawa yakeyi saboda wahala,kuma doctor tana fitar da wani ruwa Mai kauri kamar an kwaba Madara A kullum sai ta ganshi d kadan yake fita Amman yanzu musamman idan tazo wajen yunkurin Amai sai ya fito da yawa Amman kuma bashi da warin komai don Allah doctor A taimaka Muna gdy da kulawa.
Amsa
Zanje kai tsaye zuwa ga tambayar ki ta biyu saboda ta farko munyi rubutu masu yawa akan wannan matsalar, ku duba link a ƙasa cikin "Rubutu Masu Alaƙa" ko kuma kuyi searching da kalmar "Laulayi".
Zubar farin ruwa mai kauri daga gaban mai ciki yakan iya zama alamun yeast infection ko kuma vaginal candidiasis. Wannan ruwan wani lokaci yakan iya zuwa har da ƙaiƙayi ko kuma wurin yayi jaa. Mata masu sabon ciki suna kan haɗarin samun vaginal candidiasis saboda raunin garkuwar jiki da suke samu a lokacin da suka ɗauki.
Allah Maɗaukakin sarki yana rage karfin garkuwar jikin mace a lokacin da ta ɗauki ciki domin ta iya jure cikin da ta samu ba tare da garkuwar jikinta ta yaƙe abinda ke cikinta ba, saboda shi ma abinda ke cikinta foreign body ne, baƙo ne, tunda yana ɗauke da wani sashe na babanshi. Wannan raunin garkuwar jiki shi zai baiwa kananan kwayoyin cuta kamar irin su yeast, malaria su rinƙa yiwa mace tsageranci suna damun mace mai ciki akai-akai.
Yadda ake maganin wannan yeast infection ko candidiasis shi ne zaki je asibiti a baki maganin da zaki dinga inserting ko kina shafawa, cikin yan kwanaki zai daina.
Haka kuma mata masu fama da yawan cutar candidiasis ko yeast infection, ana basu shawarar yawan shan madarar yoghurt. Dalili kuwa shi ne, madarar yoghurt tana É—auke da wasu bakteriya da ake cewa lactobacillus. Wannan bakteriya ta lactobacillus tana zama ne a gaban mace kuma tana bada kariya sosai ta hanyar korar kwayoyin cutar yeast da hanawa sauran miyagun kwayoyin cuta zama a gurin.
Bugu da ƙari, wannan bakteriya ta Lactobacillus tana samar da sinadarin Lactic acid a gaban mace, wannan sinadarin lactic acid yana maida wurin acidic environment, duka saboda kar miyagun kwayoyin cuta su samu gurbin zama.
Akwai kuma wani normal abu da zai iya sa mai ɗanyen ciki ta kama ganin zubar ruwa, ana kiran sa leucorrhoea of pregnancy. Amma wannan ruwan normal discharge ne da masu ciki ke samu bayada kauri ko ƙaiƙayi, yana zuwa tamkar normal discharge din da mata ke samu kamin suyi ciki, amma idan sun yi ciki yana ƙara zuwa da yawa. Hakan yana ɗaya daga cikin alamomin samun ciki da ke fara bayyana.
Fannin Mata