Kalolin Abincin Da Ke Tayar Da Ciwon Gabobi Na Rheumatoid Arthritis

Assalamu alaikum. Dr. barka da rana Dr. Ya aiki? Dan Allah inada tambaya ne. Ina fama da rheumatoid arthritis ne to game da abincin da ciwon ba ya so ina ƙoƙarin kiyayewa amma har ynzu ina samun ciwo kusan duk abun da naci (abinci). Ina neman shawara da ƙarin bayani.

 

Ciwon gabobi


Amsa

Wa alaikumus salam, ciwon rheumatoid arthritis (RA) yana da alaĆ™a ne da kumburi da jin ciwon gabobin jiki, musamman Ć™ananan gabobin jiki na hannaye, kuma tabbas nau'ukan abincin da mutum yake ci ko yake sha suna iya yin tasiri wajen tada ciwon ko ta'azzara ciwon a lokacin fa ya taso. 

Duk da kasancewar kin ce komai kika ci ko kika sha, yana ƙara miki jin ciwon jiki da gabobi ne, toh, ai ba zai yiwu ki zauna babu cin abinci ko shan abin sha ba. Abinda ya kamata kiyi shi ne kiyi ƙoƙarin lura da nau'in abincin da idan kika ci ko kika sha, yana ƙara ta'azzara miki jin ciwon jiki. Daga nan sai ki daina cin kalar wannan abin ci ko shan sa. Wannan shi ne ake kira da "Diet modification" a likitance. Sauran abubuwan da ya kamata kiyi sune:

1. Ki rage yawan yin amfani da madara (dairy foods), da alkama (wheat), da kayan yaji (spicy foods), da kayan gwari (nightshade vegetables) kamar kayan miya da dankali musamman idan kika lura cewa yin amfani dasu yana kara miki jin ciwon gabobi.

2. Ki yawaita ci da shan abubuwa masu rage ƙiba da kumburin gabobi (anti-inflammatory foods), kamar kifi, ko ganyayyaki, ko ya'yan itace, ko ganyen shayi.

3. Ki yawaita shan isasshen ruwa domin yana wanke koda kuma yana taimakawa wajen tsaftace jinin jiki daga tarkacen abincin da ya narke.

4. Ki kaucewa ci da shan abubuwa masu haddasa kumburin gabobi ko karin kibar jiki, kamar abubuwan da ke da auke da sugar sosai, ko kayan gwangwani (processed foods), ko lemun kwalba ko lemun gwangwani (soft drinks), ko naman shanu da raguna (red meat), ko abubuwan da aka soya da mai (deep-fried foods).

5. Ki riƙa samun isasshen hutu (enough rest), tare da yin ayyukan motsa jiki (physical exercises).

6. Daga karshe, ki riƙa ƙoƙarin zuwa asibiti domin ganin likitanki da zarar kinji yanayin jikinki ya canza. Allah SwT ya baki lafiya, amin.

Wanda ya amsa tambayar: Dr. Usman Shehu Hassan 


Rubutu Masu Alaqa

1. Yadda ake Maganin Ciwon Baya ta Hanyar Motsa Jiki

2. Meke Kawo Ciwon Baya Bayan Aikin Tiyatar Cire Jariri CS

3. Ciwon gwiwa da yadda ake maganinshi (Knee Osteoarthritis)

4. Shin Matsala Ne Dawowar Ruwan Maniyyin Mijina Bayan Mun Gama Saduwa?