Matsaloli Da Alamomin Karancin Jini Ga Mata Masu Ciki


Karancin jini, wanda ake kira da "anemia" a  harshen turanci, na É—aya daga cikin matsalolin da ke addabar mata masu ciki, musamman a wannan zamani da muke ciki, kuma wannan matsala ce da zata iya shafar lafiyar uwa da abin da ke cikin ta idan ba a kula da wuri ba. 

Wannan matsalar Æ™arancin jini tana faruwa ne lokacin da jini yake dauke da Æ™arancin  sinadarin haemoglobin. Sinadarin haemoglobin shi ne sinadari mafi amfani a cikin jini, domin shi ne yake da alhakin É—auka da zagayowar iskar oxygen da muke shaÆ™a da kuma duk wani abinci da muke ci zuwa ga sauran sassan jiki.

Alamomin Karancin Jini


Mata masu juna biyu suna buÆ™atar chin abubuwan Æ™arin jini saboda jikin su ya samar da isasshen jini don biyan buÆ™atun uwa da jaririn dake cikin ta. Idan mace bata samun isasshen sinadarai kamar su iron, folic acid, da vitamin B12 a abincin ta, hakan na iya haifar da Æ™arancin jini. 

Alamomin Karancin Jini Ga Mata Masu Ciki 

Likitoci suna cewa mace mai ciki 'yar Afrika tana da ƙarancin jini a lokacin da gwajin PCV nata yayi ƙasa da kashi 30 a cikin ɗari (<30%) ko kuma mace ta nuna wasu alamomin ƙarancin jini. Ba ga mata masu ciki kaɗai ba, ƙarancin jini a jiki yana nuna alamomi kamar haka;

  • Yawan gajiya mara misaltuwa ba tare da anyi aiki mai yawa ba
  • Kasala
  • Daukewar numfashi ko numfarfashi sama-sama
  • Jiri
  • Ganin juwa 
  • Karin hasken tafin hannu da Æ™afafu
  • Kumburin kafafu
  • Yawan ciwon kai
  • Bushewa da kara hasken fata

Illolin Karancin Jini Ga Mata Masu Ciki 

Matsalar rashin jini na da matuƙar haɗari, musamman idan tayi tsanani ga mata masu ciki. Karancin jini ga mai ciki yana haifar da illoli dayawa ga uwa da jaririnta, kaɗan daga cikin illolin da zai iya haifar ma uwa sun haɗa da:

  1. Zubewar ciki 
  2. Tasowar nakuda kamin yaro ya isa haihuwa (preterm labor)
  3. Haihuwar bakwaini (preterm delivery)
  4. Zubar jini dayawa bayan haihuwa 
  5. Rashin karfin jiki
  6. Karancin ruwan faya

Haka shi ma jaririn da ke ciki yana iya samun waÉ—annan matsalolin 

  1. Jinkirin girma saboda rashin samun wadataccen jini daga mahaifiya (IUGR)
  2. Mutuwa a ciki (IUFD)
  3. Rashin nauyi ga jariri (LBW)
  4. Haihuwar jariri da naÆ™asa 
  5. Haihuwar jariri da ƙarancin jini
  6. Jinkirin girma da wayon jariri bayan haihuwa (Developmental delays)

Hanyoyin Kare Mata Masu Ciki Daga Samun Karancin Jini 

Hanyoyin da za a iya ɗauka don gujewa wannan matsalar karancin jini ga iyayen mu mata masu ciki suna da yawa. Mafi muhimmanci shi ne chin abinci mai gina jiki kamar irin su nama, kifi, wake, da chin kayan marmari kamar su ayaba, da amfani da ganyayyaki kamar su alayyahu, lettuce, salad da dai sauransu. Wannan yana taimakawa mace ta samu isasshen iron da folate waɗanda zasu taimaka da ƙarin jini a jikinta.

Likitoci na rubuta magungunan ƙarin jini ga mata masu ciki a lokacin zuwa awo, ko da suna da isasshen jini a jikin su. Saboda haka wajibi ne ga duk mace mai ciki, ta riƙa shan waɗannan magungunan kullum daga lokacin da tasan tanada ciki har makonni shida bayan haihuwa domin gujewa wannan matsala ta karancin jini. Magungunan su ne kamar haka;

  • Folic acid (Ƙaramin magani ne kalar ruwan Æ™wai, yellow)
  • Iron (Magani ne mai kalar jaa)

Waɗannan su ne magungunan da aka fi amfani dasu, ga su da arha da sauƙin samu, ga kuma matukar muhimmanci. Amma ana iya samun wasu magunguna na ruwa ko na tablet da ke ƙunshe da wadannan sinadaran, suma likitoci na rubuta su, sai dai galibi sun fi waɗannan tsada.

Yana da mahimmanci a riƙa shan waɗannan magunguna tare da abinci mai kyau domin inganta tasirin su. Kuma idan mace ta lura da alamomin rashin lafiya, kamar yawan gajiya ko tashin zuciya, ya kamata ta garzaya wajen likita domin a tabbatar da matsalar kafin ta tsananta.

Kammalawa

Rashin jini matsala ce da ake iya shawo kanta idan aka É—auki matakan da suka dace. Domin haka, kula da lafiyar mace mai ciki ya zama wajibi ko ba don kula da lafiyarta kaÉ—ai ba, har ma don lafiyar jaririn da ke cikin ta. Rashin jini ba matsala ce da za a raina ba, kuma maganinta yana farawa ne daga kyakkyawan shiri na abinci da kulawa da lafiya.


Rubutu Masu Alaƙa

1. Alamomin Nakuda: Yaushe Ya Kamata Mace Mai Ciki Taje Asibiti Haihuwa

2. Yadda Ake Gane Kwanciyar Jariri A Cikin Mahaifa

3. Bayani Game Da Ruwan Nono Mai MaiÆ™o Ga Mai Shayarwa 

4. Alamomin Shigar Ciki: Ya Mace Take Gane Tanada Ciki?