Saboda yadda naga da dama mata na yawaita tambayar yaushe ne ya kamata mace tayi gwajin ciki da kuma yadda ake gwajin ciki da tsinke (PT Strip)? Na ga ya dace na ɗan yi ƙarin bayani saboda sabbin amaren da muke samu a kullum, tun daga December hat zuwa yau.
Mafi kyawun lokaci yin gwajin ciki shi ne bayan lokacin da kika yi É“atan wata, ma'ana lokacin da kike tsammanin zuwan al'adar ki ya shuÉ—e kuma al'adar bai zo ba. Alal misali, idan kina tsammanin sake ganin al'adar a wani takamammen lokaci, ranar farko bayan wannan lokaci ya wuce zai iya zama lokacin da zaki iya yin gwajin ciki da tsinke.
Amma duk da haka, idan kika yi haƙuri ki ka jinkirta tsawon sati ɗaya bayan ranar da al'adar ki ya kamata ya zo amma bai zo ba, a irin wannan lokaci zaki fi samun sakamako mafi inganci (reliable).
Dalili kuwa shi ne sinadarin hormone na hCG (wanda shi ne ake gwadawa don gane akwai ciki ko babu) yakan fara ƙaruwa a cikin jini tun daga lokacin da aka samu ciki zai cigaba da hauhawa har zuwa haihuwa. Saboda haka, idan kika yi gwajin ciki da tsinke a lokacin da sinadarin bai da wani yawa a cikin jini, akwai yiwuwar ki samu saɓanin sakamakon gaskiya.
Duk da cewa tsinken gwajin ciki na fitsari sun ɗan bambanta, wasu sun fi wasu saurin ganowa, akwai tsinken da zai iya gane ciki ma tun kafin mace tayi ɓatan wata. Amma komai saurin ganewar tsinke an fi so a bari sai bayan aƙalla kwana shida ana jiran zuwan jinin al'ada amma bai zo ba.
Yadda ake ake gwajin ciki da tsinke
Idan za ki yi gwajin ciki da tsinke a gida, yana da kyau ki yi shi da safe musamman lokacin da kika farka daga bacci, kiyi amfani da fitsarin farko da zakiyi (ma'ana fitsarin da ya kwana a cikin marar ki) domin a wannan lokacin sinadarin hCG yana da yawa a cikin fitsarin ki, musamman idan ba ki sha ruwa sosai kafin ki kwanta ba. Wannan zai taimaka wajen samun sakamako mafi inganci.
Daga nan zaki iya samun wani kwalba, ko roba ko kofin glass sa kiyi fitsari a cikin sa. Daga nan sai ki ɗauko tsinken ki na gwaji ki tsoma a cikin fitsarin ki barshi a ciki kamar na daƙiƙa biyar zuwa goma (5-10 seconds) sannan sai ki zare ki ajiye har ya bushe na mintuna biyar zuwa goma sannan ki karanta.
A lura cewa, idan an buɗe tsinken gwajin ciki na fitsari ana riƙe wurin da ke da kala ne (akwai tsinke masu kalar ja, akwai kalar kore, akwai kuma bula). A cikin kalar an rubuta HCG da farin tawada, to wannan ƙarshen ne ake riƙewa sai tsoma wancan ƙarshen a cikin fitsari.
Idan muka lura zamu ga sashen da ake tsomawa a cikin fitsari yana da wani layi baƙi babba da kuma wasu arrows (layuka biyu masu kama da kibiya). Toh ba'a son idan an tsoma tsinken a cikin fitsari ya wuce wannan babban layi.
Wasu kuma sukan sanya tsinken a cikin fitsari kai tsaye a lokacin da suke yin fitsarin, hakan shi ma babu matsala. Kawai dai a tabbata cewa sashen da ya kamata a tsoma cikin fitsari toh shi ne fitsarin ya taɓa.
Yadda ake gane sakamakon gwajin ciki na tsinke da fitsari
Idan kuwa ba layi jaa da ya fito, ko kuma layin da ya fito yana kusa da sashen da kika tsoma a fitsari, kamar yadda zamu iya gani a hoton da ke sama, to wannan gwajin bayada inganci, ko dai anyi kuskure wurin yin gwajin ko kuwa tsinken da mace tayi amfani dashi ya lalace, saboda haka sai an sake gwaji.
A wani lokaci, musamman idan mace tayi saurin yin gwajin jim kaɗan bayan tayi ɓatan wata, zata iya samun layi biyu jajaye sun fito amma ɗayan bai fito da kyau ba, kamar yadda zamu gani a hoton da ke kasa, wannan yana nuna akwai ciki, amma ƙarami ne sosai.
Masu nema Allah ya basu, waɗanda suka samu Allah ya raba lafiya, wadanda suka samu suna neman zubar wa Allah ya shirye su. Idan wannan rubutun ya amfanar da ku, toh ku taya mu yaɗawa, wasu suma su amfana, musamman sabbin amaren nan namu, wannan rubutu sadaukarwa ne gareku amaren December.😂
Rubutu Masu Alaqa
1. Mene ne Ingancin Gwajin Ciki Da Gishiri?
2. Alamomin Shigar Ciki: Ya Mace Take Gane Tanada Ciki?
3. Matsanancin laulayi a farkon samun ciki da kuma yadda ake maganinsa (Hyperemesis gravidarum)
4. Gwaje-gwajen da ya kamata ma'aurata suyi kamin su ƙulla niyyar aure (Premarital screening tests)
0 Comments