A lokacin ɗaukar ciki, kwanciyar jariri a cikin mahaifa yana taka muhimmiyar rawa wajen sauƙaƙe haihuwa. A mafi yawan lokuta, jarirai suna juyawa zuwa kwanciya mai kyau, kwanciyar da kan jariri yake a ƙasa (cephalic position) a watannin ƙarshe, wato tsakanin makonni 32 zuwa 36. Wannan shi ne matsayi mafi dacewa domin haihuwa ta gaban mace, inda kansu ke kallon ƙasa, ƙafafunsu kuma suna sama.
Amma wani lokaci, jaririn na iya kasancewa a wani kalar matsayi ko kwanciya mara kyau, kamar breech position (kafafu-kasa, kai a sama) ko kuma transverse position (jariri ya gitta kwance a gefe). Wannan na iya jefa mahaifiya cikin damuwa da tunani musamman idan lokacin haihuwa ya kusa.
A watan takwas, yawancin jarirai sun kusa ƙare matsayin su, mahaifiya na iya lura da yadda jaririn ke motsi kuma ta chanke inda kansa ko ƙafafunsa suke. Idan jariri yana cikin cephalic position, ma'ana yana kwanciya daidai, mahaifiya za ta fi jin harbin ƙafafun sa a saman ciki, kusa da cikin ƙirji, saboda ƙafafun sa na sama. Haka kuma, motsin hannayen sa yana iya kasancewa a tsakiyar ciki, yayin da motsin kai kuma zai zama a ƙasan ciki.
A gefe guda, idan jariri yana cikin breech position, ma'ana yana kwanciya da kai a sama ƙafafu a ƙasan mahaifa, toh mahaifiya za ta ji motsi mai tsanani ko harbin ƙafafu a ƙasan marar ta. Haka kuma, motsin kai zai kasance a saman ciki, kusa da cikin ƙirji, wanda ke nuna cewa kansa bai koma ƙasa ba.
Amma, ba lallai ba ne mahaifiya ta tabbatar da matsayi na jariri daga motsi kawai. Likitoci da ungozoma suna amfani da hanyoyi biyu domin gano matsayin jariri matukar kina zuwa awo.
Na farko shi ne duba ciki ta hanyar da ake kira Leopold’s Maneuvers, inda suke amfani da hannunsu don gano inda kansa, bayansa, da kafafunsa suke.
Na biyu kuma shi ne amfani da hoton ultrasound (Hoton Kayan Ciki Ta Hanyar Sauti), wanda ke bada sahihin bayani game da matsayin jaririn. Wannan hanya ce mafi aminci kuma mafi inganci domin cire duk wani shakku.
Idan aka gano cewa jariri yana cikin breech position ko wata kwanciya mara kyau, akwai hanyoyin da za a iya amfani da su don taimakawa.
Yawancin jarirai suna juyawa da kansu zuwa cephalic position kafin makonni 36. Amma idan hakan bai faru ba, likita na iya amfani da dabarar external cephalic version (ECV), inda zai juya jaririn daga waje ta hanyar amfani da hannun sa domin mayar da jaririn a cephalic position.
Wannan hanya tana da matukar amfani, amma likita kwararre a gefen mata (Obstetrician) ne kaÉ—ai ne zai iya yi bayan an tabbatar cewa yin haka ba zai haifar da wata matsala ga mahaifiya ko jariri ba. Sannan akwai sharuddan da dole sai an cika su kafin ayi tunanin yin wannan juyin.
Idan jaririn bai juya ba har lokacin haihuwa, likitoci za su ba da shawarar hanyar haihuwa mafi aminci ga mace, wanda yawanci zai iya zama ta hanyar tiyatar (cesarean section) domin gujewa haÉ—ari.
A ƙarshe, yana da matukar muhimmanci mace mai ciki ta dinga zuwa awo duk lokacin da aka tsara na duban ciki (antenatal visits). Wannan yana taimakawa wajen gano idan akwai matsalar kwanciyar jariri da wuri, kuma likitoci za su iya ba da shawarwari na musamman idan akwai wani abin da ya za'a iya yi.
Ko da kuwa jariri akan kwanciya mara kyau, da yawa daga cikin waÉ—annan matsalolin ana iya warware su kafin haihuwa, domin likitocin mata suna da hanyoyi masu kyau da kuma kwarewa wajen kula da irin waÉ—annan yanayi. Mahimmanci shi ne samun kwanciyar hankali da bin duk wani shawara da likitocin ki suka bayar.
Idan wannan rubutun ya amfanar daku, toh ku taya mu yaɗa wannan saƙon domin wasu suma su amfana.
Rubutu Masu Alaqa
1. Alamomin Nakuda: Yaushe Ya Kamata Mace Mai Ciki Taje Asibiti Haihuwa
2. Budewar Gaban Mace Da Kuma Yadda Yake Samun Kari Yayin Haihuwa