Zubar Farin Ruwa Mai Kauri Daga Gaban Namiji

Matsalar prostate


Assalamu alaikum Dr. Don Allah ina neman karin bayani, ina samun zubar farin ruwa mai kauri (kamar sperm) daga gabana, a lokacin da nake yunkurin bahaya. Nagode.

Zubar farin ruwa mai kama da sperm daga gaban namiji a lokacin bahaya (musamman idan ka yi nishi sosai) na iya zama alamar wani abu a cikin tsarin jikin ka, kuma yana da kyau a fahimci dalilin hakan. Ga wasu abubuwan da zasu iya kawo wannan matsala:

1. Matsalar Infection na Gland É—in Prostate (Prostatitis):

Wannan yana faruwa ne idan gland É—in prostate (wanda ke kusa da mafitsara) ya kamu da kwayoyin cuta ko infection.

Yana iya sa ruwa mai kama da maniyyi ya fita lokacin da kake aikin da ke buƙatar yunƙuri, kamar bahaya. Wannan yawanci ba ya tare da wari, amma yana iya zuwa tare da:

  1. Ciwon mara ko gadon baya.
  2. Wahalar fitsari.
  3. Jin kasala a yankin ƙasa.
  4. Zubar ruwa mai kauri bayan gama fitsari 
Wannan zubar ruwa mai kauri da matsalar prostatitis ke kawowa, yana raguwa a lokacin da mai matsalar ya sadu da iyalansa ko ya fitar da maniyyi ta kowace irin hanya. Dalili kuwa shi ne, gland din prostate shi ke samar da wannan ruwa mai kauri da ake fitarwa a lokacin kawowa, su kuma tantanin halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi suna fitowa ne daga ya'yan maraina, sai su gauraye su fito yayin kawowa.

Saboda haka, a lokacin da mutum yayi inzali zai lura da cewa zubar ruwan ya ragu sosai ko ma ya daina na É—an wasu kwanaki, kamin daga baya ya cigaba idan ba'a je akayi magani ba.

2. Rashin Daidaituwar Tsarin Hormones:

Idan hormones da ke sarrafa gland É—in reproductive system ba su daidaita ba, gland É—in prostate na iya fitar da ruwa fiye da yadda ya kamata. Wannan na iya faruwa ba tare da wata cuta mai tsanani ba.

3. Girman Prostate (Benign Prostatic Hyperplasia - BPH):

Yana iya faruwa ne a wasu maza, musamman tsofaffi, inda prostate ke girma fiye da ƙima, sannan ya fara shaƙe bututun fitsari. Wannan ma yana sa ruwa mai kama da maniyyi ya riƙa fita. Haka kuma zai zo da sauran alamomin matsalar prostate kamar haka;

  1. Yin fitsari guntu-guntu
  2. YunÆ™uri yayin fitsari 
  3. Rashin fitowar fitsari har sai anyi yunkuri 
  4. Rashin fitowar fitsari da Æ™arfi 
  5. Yawan fitsari akai-akai
  6. Jin wani fitsari nan take bayan gamawa

4. Inzali koma baya (Retrograde Ejaculation):

Wannan yana nufin cewa lokacin da mutum ke yin inzali, wani sashe ko duka ruwan maniyyi yana komawa a cikin mafitsara maimakon fita waje ta hanyar da aka saba a bututun fitsari. Wannan yana iya haifar da ganin irin wannan farin ruwa a lokacin fitsari tare da sauran alamomi kamar haka:

  1. Rashin kawowa bayan mutum ya kai ƙololuwar jima'i (Dry orgasm)
  2. Fitar ruwan maniyyi É—an kaÉ—an yayin inzali

5. Matsalar Tsokokin Mara (Pelvic Floor Dysfunction):

Idan tsokokin da ke kula da riƙe fitsari da bahaya ba su da ƙarfi, suna iya sa gland ɗin prostate ta fitar da ruwa lokacin da ka yi yunkuri.

6. Ciwon Infections ko Cututtuka:

Cututtukan da ake samu ta hanyar saduwa (STIs), kamar su cutar Gonorrhoea da Chlamydia suna kan gaba wajen haifar da irin wannan zubar ruwa daga gaban namiji. Amma suna haifar da zubar ruwa ne ba sai lokacin yunkuri ba, kuma mafi yawanci irin wannan ruwan yana tare da wani wari, kaikayi, jin ciwo yayin fitsari ko rashin jindaÉ—i.

Abin Da Ya Kamata Ka Yi

1. Ka Je Asibiti:

Gwajin asibiti na jini, fitsari, ko na jini, ko hoton ultrasound, ko gwaje-gwajen cututtukan saduwa na iya taimakawa wajen gano asalin matsalar. Likita na iya bada shawarar a yi gwaje-gwajen domin tabbatar da cewa babu infection ko cuta.

2. Ka Lura Da Alamomi 

  • Lura da wasu alamomi kamar irin;
  • Jin zafi yayin fitsari
  • Jini a fitsari ko a ruwan maniyyi
  • Zazzabi ko kasala
  • Wahalar fitsari
  • Yawan fitsari akai-akai 
  • Rashin fitowar fitsari da Æ™arfi 
  • Rashin fitowar ruwan maniyyi bayan an yi inzali.
  • Haka kuma, ka lura da lokacin da ruwan ke zuba, yana fitowa ne yayin yunkuri ko haka kawai, ka lura da kalar ruwan da ke fita.

3. Ka Guji Sakaci

Kada ka yi amfani da magunguna ba tare da likita ya tabbatar da matsalar ba, ko kuma ka fara shan maganin gargajiya da sunan maganin sanyi, wannan duk yana daga cikin sakaci da kuma isgili da lafiya.

Kammalawa

Fitowar wannan ruwa mai kauri bayan fitsari na iya kasancewa al'ada a wasu lokuta, musamman ga gwauraye, amma sai idan ruwan basu fitowa da wasu matsaloli irin waÉ—anda muka ambata a sama. Amma idan fitar ruwan ya zama mai yawa ko yana tare da wasu matsaloli, yana da kyau ka je asibiti don likita ya duba ka sosai. Kula da lafiya yana da muhimmanci.