Abubuwan Da Ke Kara Girman Ciki Ga Mace Mai Juna Biyu

Girman ciki


Girman ciki na É—aya daga cikin abubuwan da mata masu juna biyu kanyi amfani dashi na tabbatar da suna É—auke da lafiyayyen ciki a zahiri. Ciki na É—aya daga cikin abubuwan da ke canja yanayin tsarin jikin mace daga lokacin da ta dauki ciki har zuwa yan watanni bayan haihuwa.

Akwai wasu daga cikin sassan jikin mace da ke samun canje-canje sanadiyar daukar ciki dan haka za mu yi bayanin kaÉ—an daga cikin dalilai dake haifar da girman ciki ko rashin girman ciki wanda da dama hakan bai zama alama ta matsala ba. 

Ga kaÉ—an daga cikin dalilan da na fito dasu waÉ—anda ke da nasaba da girman ciki ko akasin hakan.

1. Yawan Ruwan Mahaifa

Ruwan mahaifa na da nasaba da girman ciki, idan mace na da yalwa ta ruwan mahaifa cikin ta zai yi girma sosai, hakan kan iya sa a kasa bambance girman ciki da kuma tsufan sa, za aga mace da ciki mai watanni 4 a amma a zahiri girman cikin kamar yakai watanni 6.

2. Yanayin Taswirar Jikin Mace

Yanayin tsarin jikin mace na da alaƙa da girman ciki ko akasin hakan, mata da ke da tsayi, ƙiba, gajarta da faɗin jiki za su iya sa a samu girman ciki sosai ko kuma akasin hakan.

3. Yanayin Jikin Jaririn Da Ke Ciki 

Idan ya zamana mace na dauke da tagwaye zai iya zama alama a fahimci hakan ta girman ciki. Haka kuma yanayin kwanciyar jariri da juyawar sa kan canja yanayin girman ciki la'akari da yanayin halittar mutum gaba É—aya.

4. Tsufan Ciki

Haka tsufan ciki na É—aya daga cikin abubuwan da ake amfani dashi a ga buÉ—ewar ciki da baya, saukar sa a mara na daga cikin abubuwan da za a ga yanayin ciki ya canja ko dai yai tsini ko Kuma ya danne mara sosai, Haka kuma a bangaren girman jikin sa.

Dan haka abinda ke da amfani shi ne a tabbatar da lafiyar ciki ta hanyar amfani da hanyoyin zamani na hoto.