Abubuwan Dake Kawowa Mata Daukewar Sha'awar Namiji Ko Rashin Jindadin Saduwa

Karancin sha'awa ga mace


Karancin Sha'awa Saboda Rashin Daidaituwar Sinadaran Hormones A Jikin Mace

Karancin sinadaran hormones na jima'i da sauye-sauyen halittar mace (female sex hormones) na iya haddasa dallashewar sha'awar mace. Alamomin karancin sinadarin su ne: jin zafi wajen jima'i saboda rashin zubar ruwan ni'ima a gaban mace, jinin haila mai wasa, karuwar jin zafi yayin fitsari da cututtukan mafitsara (UTIs), yawan É“acin rai ba gaira ba dalili, ciwon nono, zubar ruwan nono, ciwon kai, ciwon damuwa, kasala, wuyar lura ko nazarin, da dai sauransu. 

Abubuwan da kan iya haddasa ƙarancin sinadaran sun haɗa da: cutar PCOS, tsananin motsa jiki ko rashin motsa jiki, rashin bacci , rashin cin abinci saboda tsoron yin ƙiba da dai sauransu. Haka kuma, ga mata waɗanda suka haura shekara 40 ƙarancin sinadaran na iya zama alama ne cewa sun kusa daina yin jinin al'ada. Don haka sai aga likita domin magance matsalar ko a nemi magani.

Budewar gaban Mace

Rashin tsukakken gaba yanda zai damƙi azzakari da kyau domin samar da jin ɗanɗanon fata-da -fata a matse. Buɗewar gaba ƙalubale ne da ke sanya raguwar jindaɗi a tsakanin ma'aurata. Sau da yawa ma'auratan biyu ba za su sami gamsuwa ba da kyau, sannan macen baza ta iya kai ƙololuwar jindaɗi ba (orgasm). Akwai salon kwanciya da magunguna na zamani da zasu iya magance wannan matsala ta budewar gaban mace

Kaciyar Mata

Kaciyar mata (female circumcision) wadda wanzami yake yanke belin mace (clitoris) da yawa fiye da yanda ya dace. Yin hakan na daÆ™ushe sha'awar mace idan ta girma. Da yawa mata ana yanke musu sha'awa a duniya tun lokacin da suke jarirai. Wasu mutane a al'adunsu suna yanke beli ne kaÉ—an, wasu kuma kamar rabi ne ake fillewa, wasu kuma cire shi suke duka, wato yanke shi suke ga baki É—aya. 

Yanke beli dayawa ko duka matsalace dake hana mace jindaÉ—in saduwar aure ko jima'i kwata-kwata, domin kuwa beli (clitoris) shi ne hedkwatar jindaÉ—in jima'in mace. Kamar yadda dai malamai su ke ta bayani cewa yin kaciyar mata mustahabbi ne a Musulunci. 

Shari'a kuma tayi nuni da cewa ka da a wuce gona da iri wurin yankan, ba kamar yanda wasu wanzamai ke aikatawa ba yanzu. To sai a nemi bayanan malaman sunnah domin fahimtar mas'alar baki É—aya. Bugu da kari, za'a iya neman magani domin inganta jindaÉ—in saduwar aure. 

Shan Wasu Magunguna 

Ko shakka babu akwai nau'o'in magungunan turawa ko gargajiya da suke iya daÆ™ushe sha'awar 'ya mace, misali magungunan da ake bayarwa domin rage ciwon damuwa ko tsananin É“acin zuciyar mutum (antidepressants) da sauransu. 

Kina mamakin cewa ada kina da sha'awa amma yanzu shiru ne? tohm yana yiwuwa waÉ—annan magungunan da kike sha wata da watanni ne, ko cikin satin nan, su ne ke sace miki sha'awa. Yana da kyau duk maganin da aka bawa marar lafiya a asibiti ko wani wuri yasan muhimmai daga cikin matsalolin da maganin ke iya kawo wa ("side-effects" nashi) don kada wani abu ya dame shi bai san abin da ya ja masa ba. 

Rashin Cin Abinci Mai Lafiya

Idan mace ba ta samun cin abinci mai kyau ta Æ™oshi wanda zai inganta lafiyarta da jikinta da sinadarai na ni'ima, to sha'awarta tamkar shuka ce wadda ba ta samun ruwa, wadda za ta mutu. Kifi, naman kaza, madara, madarar yogort, hanta, Æ™wai, zuma, dabino, aya, gyaÉ—a, kankana, aiba da sauran abincin mai gina jiki da kuzari tare da 'ya'yan itatuwa zasu iya cika mace da sha'awa da ni'ima bayan É—aukewar sha'awa. 

WaÉ—annan abubuwan marmari da abinci tamkar taki ne da ruwa ga shuka, wato sha'awar 'ya mace. Don haka mazaje su siyama matansu kayan dadi domin moruwa daidai gwargwadon hali.

Saurin Kawowar Maigida

Wannan matsalar na da alaÆ™a da mazan aure kai tsaye. Wannan matsalar na cutar da mata sosai kuma wani lokacin tana da alaÆ™a kai tsaye da rashin Æ™arfin. Idan akwai karfin mazakuta ga namiji ko da azzakarin ba babba ba ne zai iya gamsar da iyalinsa idan akwai Æ™arfi sosai, kuma zai daÉ—e yana saduwa da iyalinsa har ta biya buÆ™atar ta. 

Haka kuma idan muka kalli matsalar ta wani mahangar, zamu iya gane cewa hakan na faruwa ne saboda rashin sha'awar namiji - wato sinadaran hormones na jima'in sa (sex hormones) sun ragu ko sunyi ƙasa, ko kuma hawan-jini ko ciwon-suga su ke haddasa masa matsalar ko ma yawan sinadarin kolesterol ko wasu matsalolin zagayawar jini duk zasu iya taruwa su daƙushe wa namiji mazakuta.

Don haka cin abinci mai inganta lafiya da harkar saduwa ko magani mai kyau da likita yayi izinin ayi amfani dashi zai iya gyara matsalar. Mafi yawan lokuta mata na bukatar tsawon lokaci kamin su kawo (ma'ana kamin su kai ƙololuwar jindaɗi saduwa / orgasm) saɓanin lokacin da maza da dama ke iya jurewa su biya musu buƙatar. Don haka, yin wasannin motsa sha'awa na tsawon lokaci (foreplay) na iya fansar lokacin da maigida ba ya iya kaiwa.

Rashin Fahimtar Yanayin Mace Da Abinda Take So Yayin Saduwa

Ko wace mace da irin buÆ™atun ta na jima'i ko saduwa, ko wace mace akwai irin abinda take so ayi mata da nau'in kwanciyar da take jindaÉ—in ta amma dayawa mata kunya na hana musu bayyana abinda suke so, don haka sai su bar mazan su cikin duhu su na ta Æ™oÆ™arin jarraba abubuwan da basa yi musu. 

Saboda haka ana son matan aure su fidda kunya domin tattaunawa da mazan su akan abin da suke so wajen jima'i da kwanciyar aure tare da mazan su, suma mazan su bayyana irin buÆ™atun nasu domin fahimtar juna da jindaÉ—in rayuwar auren su. 

Haka kuma yana da kyau maigida ya rinÆ™a lura da yin nazari akan buÆ™atun wasu sassan jikin matar sa idan mai yawan kunya ce. Yau da gobe zai iya gane abin da yafi yimata daÉ—i wajen saduwa. Yau da gobe zaka tara ilimi mai yawa akan buÆ™atar matar ka amma idan har kana lura da kyau. 

Sabawa Da Yin Istimna'i Kamin Aure

Idan mace na wasa da farjin ta (istimna'i) da yatsa ko wani abu da ta take sakawa a ciki domin biyawa kai buÆ™ata (istimna'i ko kuma masturbation), zai iya sanya ta ji ba ta jin daÉ—in jima'i ko gamsuwa da duk wani namiji sai dole tayi istimna'in da ta saba saboda tafi kowa sanin jikin ta da mallakar sa, ta gano hanyoyin biyan buÆ™atun ta na shaiÉ—an wanda auren ta ba zai iya biya mata ba. 

Musamman a cikin mata zaurawa da 'yan mata yin istimna'i abu ne da ya zama ruwan dare, dayawan mata sun saba biyawa kan su buÆ™ata, kuma hakan zai iya shafar tarayyar su da mazan da zasu aura nan gaba. Kamar dai yadda muka yi bayani a wata wallafar mu a can baya cewa, sabawa da istimna'i yana hanawa mace gamsuwa idan tayi aure kuma yana sa mace wuyar kawowa wajen jima'i saboda koyawa jikinta da sai an taÉ“a wani sashen farjin ta don ta kawo, wanda mai yiwuwa ne azzakari baya iya taÉ“a wurin lokacin saduwa - a zahirin jima'i. 

Don haka istimna'i yana sa rashin gamsuwar saduwar aure ga mace. Duk matar da ta saba da yin istimna'i kamin aure idan tayi aure mijinta zai sha wahala wajen gamsar da ita ta hanyar azzakarin sa kaÉ—ai, dole sai ya haÉ—a da yimata irin abubuwan da ta saba yi a lokacin istimna'i. Saboda jikinta ya riga ya koya, ta riga tayi wa kanta horo. 

Zata rinÆ™a tunanin mijinta baya iya gamsar da ita saboda sabon da tayi da koyawa jikin ta hanyar gamsar da kanta fiye da hanyar da ta dace da É—abi'a, watau hanyar jima'i a cikin sunnar aure. Mai istimna'i ta canza É—abi'ar ta. Da yawa zaka samu cewa mata masu yawan istimna'i basu jin daÉ—in jima'i sai istimna'in nan kawai, koma basu gamsuwa sai sunyi istimna'i a banÉ—aki bayan saduwa da mazan auren su. 

Wannan zai iya kawo babbar matsala a cikin aure. Saboda sabawa da istimna'i shi ke sa wasu mata su daina sha'awar namiji baki ɗaya, wasu kuma su fara sha'awar saduwa da mata 'yan uwansu, saboda saduwa mace da mace itace za ta fi samar da haƙikanin abin da suke samu a lokacin istimna'i.

Kamuwa Da Aljanin Soyayya (Jinnil Ashiq)

Aljani na iya shiga a jikin mace da sunan yana sonta ya dinga saduwa da ita ko ma ya aureta. Hakan zai sa aljanin ya hana ta aure, ko haihuwa, ko rashin zama lafiya da miji idan tayi auren, kuma zai sa mata É—aukewar sha'awa da ni'ima ga mijin da ta aura, ko zubar jini ko ruwa mai wari ko kuma gaban mijin yaki miÆ™ewa a duk lokacin da ya kusance ta. 

Mace za ta rinƙa mafarkin ana saduwa da ita wanda shaiɗanin aljanin zai zo mata da siffar mijin ta ko wani mutum da take so, ko siffar mace yana saduwa da ita. Ko ta dinga ganin mutum tsirara a gabanta. Waɗannan suna daga cikin alamomi, kuma dalilin hana mace jin dadin jima'i ko ɗaukewar sha'awa.