
A watannin farko na rayuwar jarirai, garkuwar jikinsu ba ta da wani karfi, amma shi kuma nonon uwa da yake fitowa a wannan lokaci yana cike da sinadarai masu kare jarirai daga cututtuka kamar gudawa, mura, zazzaɓi, da sanyi. Wannan kariya ba ta samuwa a madarar roba, domin nonon uwa yana da sinadarai masu rai da ke daidaita lafiyar jarirai bisa buƙatar su ta musamman.
Me yasa dole sai watanni shida?
A wannan lokaci madarar nonon uwa kaɗai yake iya wadatar da jariri da dukkan abinci, ruwa da sinadarai da jikinsa ke buƙata. Idan jariri ya wuce watanni shida, bincike ya nuna nonon uwa kaɗai ba zai iya biya masa da dukkan bukatunsa ba.
Shayarwa ta ruwan nono zallah na har tsawon watanni shida yana taimakawa kwakwalwar jarirai ta girma da saurin fahimta, yana hana shi kamuwa da cututtuka, kuma yana sa jariri yayi lafiya fiye da wanda aka fara ba abinci da wuri.
Ba jariri kaÉ—ai ke amfana ba — ke ma uwa za ki samu amfani da yawa! Kina mamaki ne? Ƙwarai kuwa kema zaki samu la'ada, domin shayarwa na taimakawa wajen rage Æ™iba bayan haihuwa, hana ciwon nono da ciwon mahaifa, kuma yana sa mahaifa ta koma daidai da sauri.
Har ila yau, wannan shayarwa yana ƙara danƙon ƙauna, haɗin kai da soyayya tsakanin uwa da jariri, domin yana jin dumin jikin ki, yana jin kamshin ki, kuma yana samun nutsuwa da jikinki. Bugu da kari, mace mai shayar da jariri nono zallah har na tsawon watanni shida tana da ƙarancin yiwuwar samun ciki a lokacin shayarwa sama da sauran da mata da suke haɗawa yaro da wani abinci.