Meke Kawo Kumburi Da Ciwon Dasashi (Gingivitis)?

Ciwon dasashi da kumburi


Gingivitis wata cuta ce ta dasashin haƙora (gums) da ke haddasa kumburi, ja, jin zafi ko zubar jini daga dasashi, musamman yayin da ake wanke baki da buroshi. Wannan cutar mafi akasari tana faruwa ne sakamakon tara datti (plaque) da kwayoyin cuta a kan haƙora da dasashi, ko kuma jin rauni kaɗan a dasashi yayin wanke baki ko wata sabgah.

Alamomin Ciwon Dasashi Na Gingivitis

  • Kumburin dasashi da hakori.
  • Jaa da zafi a dasashi.
  • Zubar jini yayin wanke ko ciwon hakori.
  • Warin baki.
  • Hakora suna iya yin laushi ko suna rabuwa da dasashi

Abubuwan Dake Kawo Ciwon Dasashi Na Gingivitis

1. Rashin tsaftar haĆ™ora – Idan ba a wanke hakora da kyau yau da kullum datti (plaque) yana taruwa, wannan dattin ya kan zama abincin kwayoyin cuta wanda zai sa su ji dadin zama a gurin su hayayyafa har su kawo ciwon dasashi na gingivitis.

2. Ciwon sugar – Na iya rage Ć™arfin jikin mutum na yaĆ™i da kwayoyin cuta, wannan zai iya sa taruwar kwayoyin cuta kaÉ—an su kawo wa mutum ciwon dasashi na gingivitis.

3. Shan taba – Yana rage lafiyar dasashi da haĆ™ori.

4. Rashin daidaituwar hormones na mata – Mata masu juna biyu, masu jinin haila, ko masu amfani da hanyoyin hana daukar ciki na iya fuskantar ciwon dasashi na gingivitis.

5. Karancin sinadarai – Karancin sinadarin Vitamin C na iya haddasa rauni a dasashin haĆ™ori.

Yadda Ake Maganin Ciwon Dasashi Na Gingivitis:

Wanke haƙora kullum a ƙalla sau biyu a rana da buroshi da man goge haƙori mai ɗauke da sinadarin fluoride.

Kurkura baki da ruwan ɗimi masu ɗauke da gishiri a ƙalla sai ɗaya a yini. Ana iya amfani da ruwan kurkura baki da ake sayarwa (Mouth Wash).

Kurkura baki da ruwa duk bayan gama cin abinci, ko duk wani abu da zai iya laƙe ma haƙora.

Yi amfani da tsinke ko robar floss domin cire datti tsakanin haƙora.

Rage cin abinci mai zaki sosai, da kuma duk wani abinci mai lakewa haƙora (sticky food) l, musamman dadare ko a yayin da mutum zai kwanta bacci.

Lazimtar wanke baki da makilin da buroshi ko aswaki kullum kamin kwantawa bacci.

Ziyarci likitan haƙora akai-akai domin tsaftace haƙora da dasashi.

Idan aka bar ciwon dasashi na gingivitis ba tare da magani ba, yana iya rikiɗa zuwa cutar periodontitis, wanda ke iya haddasa zubar haƙora.